Dakarun Isra’ila sun rusa gidan wani Bafalasdine da ake zargi ya kai wa wani mazauni yankin da Isra’ila ta mamaye a bara.
Wata sanarwa da rundunar sojin Isra’ila ta fitar ta ce an rusa Omar Jaradat a garin Al-Silah Al-Harithiya, yammacin Jenin a arewacin gaɓar Yamma da Kogin Jordan.
Sanarwar ta nuna cewa mazauna yankin sun ta jifar sojojin Isra’ila, yayin da kuma suka mayar da martani.
Rikicin ya yi sanadin raunata wasu Falasdinawa
A watan Maris, jami’an suka tarwatsa gidaje uku na mambobin Jaradat a Silat Al Harthiya.
Isra’ila ta sha rusa gidajen mutanen da take zargi sun kai wa ƴan ƙasarta hari a Gabar Yamma da Kogin Jordan da kuma gabashin Kudus.