Sojojin Najeriya hadi dana kasar Nijar karkashin rundunar hadaka ta MNJTF sun kaiwa kungiyar Boko Haram hari a maboyarsu dake dajin Sambisa.
Sun kashe ‘yan Boko Haram 20 inda su kuma a bangarensu, suka kashe soja daya.
An yi gumurzunne a yankin Tumbun Fulani da Tumbun Rago.
Kakakin rundunar sojojin, Ndjamena, Col. Muhammad Dole, ya bayyana cewa, bayan ganin sojojin, ‘yan Boko Haram din sun tsere suka bar makamansu.