Dakarun Najeriya da ke da alaka da birgediya ta 34 sun kashe wani dan bindiga da aka bayyana amatsayin Kwamandan masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) a Imo.
Sojojin sun ce sun ci karo da ‘yan kungiyar ‘yan awaren, inda suke ta harbe-harbe a mahadar ayaba da ke karamar hukumar Orlu a jihar.
An ce suna aiwatar da umarnin “zama-gida ba bisa ka’ida ba” kan ‘yan ƙasa masu bin doka.
Kakakin rundunar, Brig.-Gen. Onyema Nwachukwu, ya bayyana a cikin wata sanarwa a Abuja ranar Litinin cewa an kashe dan bindigar ne a yayin wata fafatawar da aka yi a yankin Ihioma a Orlu.
Nwachukwu ya ce a lokacin da suka ga sojojin, ‘yan kungiyar IPOB/ESN sun janye a cikin wata babbar mota kirar Toyota Highlander blue zuwa yankin Ihioma domin karfafa musu gwiwa.
A rikicin da ya barke, an damke daya daga cikin masu laifin, yayin da wasu suka gudu cikin rudani. Dakarun na ci gaba da yin katsalandan a yankin gaba daya a ci gaba da gudanar da aikin zakulo ‘yan ta’addar da suka tsere.