fbpx
Sunday, February 28
Shadow

Sojojin Najeriya sun kashe manyan kwamandojin Boko Haram

Hukumar sojin Najeriya ta bayyana cewa ta kashe wasu manya-manyan kwamandojin Boko Haram a harin data kai a mabiyarsu dake Durbada, Borno.

 

Me kula da bangaren watsa labarai na hukumar, Majo Janar John Enenche ya bayyana cewa rundunar Operation Lafiya Dole ce ta kai harin ranar 17 ga watan Afilu.

 

Kuma an kai harinne bayan samun bayanan sirri da suka tabbatar da cewa garinne Mayakan Boko Haram din ke komawa su boye bayan kai hari.

 

Rahoton wanda ya fito daga kamfanin dillancin Najeriya,NAN ya bayyana cewa sojojin sun kuma bi masu kokarin guduwa daga garin suka kashesu a harin da aka kai ta sama.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *