fbpx
Saturday, September 19
Shadow

Sojojin Najeriya sun yi artabu da yaran Gana inda suka kashe 2 da kama 5

Sojojin Najeriya dake rundunar Operation Whirl Stroke dake yaki da ayyukan ta’addanci a yankin Arewa ta tsakiya sun farwa wata maboyar yaran Marigayi, Terwase Agwaza,  wanda aka fi sani da Gana.

 

Sojojin sun kaiwa Maboyar ‘yan Bindigar hari ne bayan samun bayanan Sirri inda kuma suka kashe 2 daga ciki tare da kama 5.

Kakakin hedikwatar tsaro ta kasa, Janar John Enenche ne ya bayyana haka ga manema labarai yace harin ya farune a Adu dake Chanchangi jihar Taraba.

 

Hakanan sojojin sun kuma kai hari a Katsina Ala dake jihar Benue inda suka kama wasu masu laifi da kwayoyi da makamai da sauransu. Yacw wanda ake zargin na fuskantar bincike inda daga baya za’a mikasu hannun ‘yansanda.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *