fbpx
Monday, March 1
Shadow

Sojojin saman Najeriya sun fitar da sunayen wadanda hatsarin jirgin sama na soja ya rutsa da su 

Rundunar Sojin Saman Najeriya ta fitar da sunayen mutane bakwai da suka mutu a cikin jirgin sojan da ya fadi a Abuja a yau 21 ga Fabrairu.

A cewar wata sanarwa da AVM Ibikunle Daramola, Daraktan hulda da jama’a da yada labarai ya fitar, ma’aikatan da suka mutu sun hada da;

1. Laftanar Haruna Gadzama

2. Laftanar Henry Piyo

3. Micheal Okpara (ATOS).

4. Bassey Etim (ATOS).

5. Olasunkanmi Olawunmi (ATOS).

6. Ugochukwu Oluka (ATOS).

7. Adewale Johnson (Onboard Technician).

Daramola ya ce Babban hafsan sojan sama (CAS), Air Vice Marshal Oladayo Amao, ya kafa kwamitin bincike don gano musabbabin hatsarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *