fbpx
Saturday, November 28
Shadow

Southampton 2-0 Everton: Everton ta fadi wasa karo na farko a wannan kakar

Kungiyar Everton ta fadi wasa karo na farko a wannan kakar bayan Southampton ta lallasa su 2-0 a gasar Premier League kuma duk da haka kungiyar ta cigaba da kasancewa a saman teburin gasar amma makin ta daidai yake dana Liverpool.

Everton ta fara barar da maki ne wannan kakar bayan sun tashi wasa 2-2 da kungiyar Liverpool a makon daya gabata, yayin da ita kuma Southampton tayi abunda ba’a taba yi ba a gasar bayan ta rama kwallaye uku da Cheldea ta zira mata ana gab da tashi wasa.
Tawagar Carlo Ancelotti sun buga wasan ne ba tare da tauraron dan wasan suna kasar Brazil ba wato Richarlison sakamakon an dakatar da shi daga buga wasanni uku.
Kungiyar Wolves da Newcastle sun raba maki bayan sun tashi 1-1 yayin da Raul Jiminez ya ciwa Wolves kwallo guda kuma bayan mintina tara shima Jacob Murphy ya ramawa kuniyar tashi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay youLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *