Yan wasan takwas ne kadai suka fi Ward Prowse cin kwallaye nesa wato free kick a gasar Premier league, yayin kwallon daya ciwa Southampton bayan Bednarek ya ci tashi kwallon ta zamo tara kuma yayi daidai da Redknapp, Nolberto da kuma Frank Lampard.
Bruno Fernandez ne ya fara ramawa United kwallo guda a wasan da taimakon Cavani wadda tasa ya zamo dan wasa na hudu da yayi nasarar ciwa Manchester kwallo a wasanni biyar wanda bana gida ba a jere.
Sai Edinson Cavani yayi nasarar cin kwallaye biyu yayin da shi kuma ya zamo dan wasa na biyu daya taimakawa Manchester United da kwallaye uku a wasa guda daga benci, tun bayan manajan kungiyar na yanzu Ole Gunnar wanda shi yaci kwallaye hudu daga benci a wasan su da Nottingham.