fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Steve Bruce da Raheem Sterling sun ce bai kamata a cigaba da buga wasannin premier lig ba har sai watan yuni ya kare

Hukumar UEFA suna fatan za’a gama buga gabadaya wasannin gasar nahiyar turai kafin karshen watan  yuli amma sai dai premier lig baza su cigaba da wasa ba sai tsakiyar watan yuni kuma da kyar su gama buga gabaday wasannin su guda 92 akan lokaci.

Manajan Newcastle Steve Bruce yace sun saurari gabadaya maganganun da aka yi, kuma zasu fara yin atisayi amma ba a kungiyance ba kamar yadda aka ace. Ya Kara da cewa shin zasu iya kai matakin da zasu yi aiki a kungiyance?, har yanzu basu da wannan amsar.
Tauraron Manchester City Raheem Sterling yace ba zai yiwu ayi atisayi na mako da rabi zuwa biyu ba sannan kuma ace wai za’a cigaba da buga wasanni, kamata yayi ace anyi atisayi na makonni hudu zuwa biyar kafin a cigaba saboda wasannin na gasa ne.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.