Bayan yankewa Mubarak Bala hukunci kan laifin da ya aikata na batanci ga Annabi(SAW) a Kano.
An samu wani lauya me sunan Mbasekei Obono ya kaiwa majalisar tarayya koke kan an cire dokar dake hukunta masu kalaman batanci ga Addini a Najeriya.
Lauyan me ikirarin kare hakkin bil’adama ya bayyana cewa, masu kalaman batancin wai suna da ‘yancin fadar Albarkacin bakinsu.
Yace idan ana son tsarin Dimokradiyya ya tabbata to lallai san an baiwa kowa ‘yancin fadar Albarkacin bakinsa.
Majalisar dai bata yi martani ba zuwa yanzu.