Yan bindiga sun kai hari wani masallaci sun kashe mai anguwa, Alhaji Abdulkadir a garin Maisamari dake karamar hukumar Sardauna a jihar Taraba.
Yan bindigar sun budewa masallacin wuta ne a sallar Isha’i amma wani abin burgewa shine wasu fusatattun masata sun kora su ba tare da sunyi garkuwa da kowa ba.
Mai magana da yawun yan sanda na jihar Usman Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin amma bai bayar da cikakkun bayanai akai ba.