fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Subhanallah:Ana caccakar mawakiya Rihanna saboda amfani da Hadisi wajan tallar kaya tsirara-tsirara

Mawakiya Rihanna na sha suka musamman a shafukan sada zumunta bayan da ta yi amfani da wata waka me suna Doom ta yi tallar kaya.

 

Wakar wadda Wani me wakar dake Landan, Coucou Chloe yayi, ya saka hadisin Annabi,Muhammadu (SAW) wanda yake magana akan alamomin tashin kiyama.

Hadisin dake cikin wakar shine Wanda Aba Huraira ya ruwai Manzon Allah(SAW) yace, Qiyama ba zata tsaya ba sai an dauke ilimi ta hanyar mutuwar manyan malamai, Girgizar kasa zata yawaita, lokaci zai rika sauri, Iftila’i zasu yawaita, kashe-kashe zai yawaita, sannan dukiya zata watsu tsakanin mutane.

 

Tun bayan sakin wakar wasu musulmai ke ta kira da a dauki mataki amma ba’a yi komai ba akai. Sai gashi yanzu mawakiyar, Rihanna ta yi amfani da ita wajan tallar kaya inda aka ga mata na yawo tsirara-tsirara.

Karanta wannan  DA ƊUMIƊUMINSA: Ƴan Boko Haram Sun Sace Naira Miliyan 82 A Yayin Harin Da Suka Kai Gidan Yarin Kuje Dake Abuja

 

Wannan lamari yasa wasu suka bayyana cewa rashin girmama addinin Musulunci ne wannan. Da kiran yayi yawa, mawakin, Coucou ya bada hakuri inda yace ya ga maganar(Hadisin) ne kawai a yanar gizo ya dauka ya saka a wakarsa ba tare da yayi bincike ba. Yace amma yana matukar bada hakuri ga duk wanda wakar ta sabawa rai.

 

Yace zai cire wakar daga duk wata kafa dan a daina jinta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.