Saturday, April 26
Shadow

Sudais ya buƙaci maniyyata su zama masu biyayya a lokacin aikin hajji

Babban limamin masallatan Harami Abdulrahman bin Abdulaziz Al-Sudais, ya buƙa ci maniyyata su zama masu bin doka da oda a lokacin gabatar da ayyukan ibadar hajji.

Shafin X na Haramain ya ambato Sheikh Sudai na kira ga maniyyatan su zama masu biyayya ga umarnin jami’an tsaro domin tabbatar da gudanar da aikin hajin cikin kwanciyar hankali da lumana.

Hukumomin Saudiyya sun ce ya zuwa ranar Lahadi kimanin maniyyata miliyan ɗaya da dubu ɗari uku ne suka isa ƙasar, don gudanar da aikin hajjin na bana.

Karanta Wannan  Hotuna: Mahajji Daga Jigawa Ya Maida Makudan Dalolin Kasar Amurka Da Kuma Riyal Na Kasar Saudiyya Da Ya Tsinta A Makka Ga Mai Shi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *