Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, ba za’a bari yankin Arewa maso yamma ya sake fadawa cikin matsalar rashin tsaro ba irin ta shekarun baya ba.
Shugaban ya kuma jinjinawa sojoji kan kokarin da suke na yakar ‘yan Bindiga musamman a jihar Zamfara.
Ya kuma nemi sojojin kada su yi kasa a gwiwa, su ci gaba da yakar ‘yan Bindigar da ci gaba da samun nasarar da suke akai.
Kakakin shugaban kasar, malam Garba Shehu ne ya bayyana haka inda yace shugaban ya lura an fara samun kwanciyar hankali a yankuna da dama na jihar ta Zamfara.
Saidai wannan na zuwane yayin da ake cikin jimamin mutuwar wasu mutane akalla 50 da ‘yan Bindigar suka kashe.