fbpx
Thursday, December 7
Shadow

Super Eagles ta tashi 1-1 da Zimbabwe a Rwanda

Super Eagles ta tashi 1-1 da Zimbabwe a Rwanda

Wanda aka sabunta Mintuna 57 da suka wuce

Tawagar kwallon kafa ta Najeriya ta tashi 1-1 tsakaninta da ta Zimbabwe ranar Lahadi a wasan neman shiga gasar Kofin Duniya da aka buga a Rwanda.

 

Tawagogin biyu sun buga wasa na biyu-biyu a cikin rukuni na uku a wasannin neman shiga gasar Kofin Duniya da za a yi a 2026 a Amurka da Canada da Mexico.

 

A minti na 26 da fara wasa ne Zimbabwe ta fara cin kwallo ta hannun Walter Musona, kuma haka suka je hutu ana cin Super Eagles 1-0.

 

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Najeriya ta farke ta hannun Kelechi Iheanacho.

Karanta wannan  Ko da za'a kwashe rabin kudin sojojin Najeriya dole a biya diyyar wadanda harim bam ya kashe a wajan Maulidi a Kaduna>>Sanata Shehu Sani

Wasa na biyu kenan da Najeriya ta tashi 1-1 a karawar cikin rukuni na uku, bayan da ta yi kunnen doki da Lesotho a Uyo ranar Alhamis.

 

Ita kanta Zimbabwe ta tashi wasan farko a cikin rukuni da Rwanda ba ci ranar Laraba.

 

Zimbabwe na buga wasanninta a Rwanda saboda ba ta da filin wasa mai darajar da za a buga wasannin.

 

Ranar 3 ga watan Yunin 2024 Super Eagles za ta karbi bakuncin Afirka ta Kudu a wasa na uku a cikin rukuni na uku.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *