fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Super Eagles za su dawo da karfinsu – Troost-Ekong ya nemi gafarar ‘yan Najeriya kan gazawarsu

Dan wasan baya na Super Eagles, William Troost-Ekong ya roki ‘yan Najeriya da su gafartawa ‘yan wasan Super Eagles na kasa samun gurbin shiga gasar cin kofin duniya na 2022 da za a yi a Qatar, ya kuma ba da tabbacin cewa tawagar kwallon kafar Najeriya za ta dawo da karfi.

Troost-Ekong wanda yana cikin tawagar da ta buga wasanta da Black Stars ta Ghana 1-1 a wasan zagaye na biyu na gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta 2022 a filin wasa na Moshood Abiola na kasa da ke Abuja a ranar Talata ya ce sun yi iya kokarinsu amma Allah bai nufa ba.

Dan wasan bayan Watford a shafinsa na Facebook ya rubuta takardar neman afuwa ga magoya bayan su sannan kuma ya gode musu da irin goyon bayan da suka ba su. Ya kuma yi amfani da damar wajen mika godiyarsa ga shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya, Amaju Pinnick, da kuma ministan matasa da wasanni, Sunday Dare bisa goyon bayan kungiyar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.