fbpx
Friday, February 26
Shadow

Surukin Rochas Okorocha ya koma Kotun Koli, yana neman a tsige Gwamna Uzodinma

Mista Uche Nwosu, ya koma Kotun Koli ne kawai bayan awanni 24 bayan da hadiman Gwamna Hope Uzodinma suka wulakanta surikin sa Rochas Okorocha saboda sake bude wani fili da gwamnatin Imo ta rufe.

Nwosu ya roki kotun kolin da ta bayyana cewa Gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Uzodinma ba dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ba ne bisa hukuncin kotun da ta ce APC da Action Alliance ne suka tsayar da Nwosu a matsayin dan takarar Gwamnan Jihar.

Surukin Okorocha wanda ya gabatar da wannan bukatar a cikin wani sabon karar ta hannun lauyan sa, Mista Philip Umeadi Jnr, ya nemi kotun da ta zartar da hukuncin akan shari’ar da aka gabatar a kan 20 ga Disamba, 2019 inda kotun ta ce jam’iyyun APC da AA ne suka tsayar da shi don haka ta bayyana nadin nasa a matsayin rashin aiki.

Nwosu yana rokon kotu da tayi amfani da wadannan bayanan da muka gabatar, don tabbatar da cewa dukkanin jam’iyyun Action Alliance (AA) da All Progressive Congress (APC) basu dauki nauyin / ko gabatar da wani dan takarar kujerar gwamnan da aka gudanar a jihar lmo a ranar 9 ga Maris, 2019 aka yanke a ranar 20 ga Disamba, 2019.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *