A karshe dai kwana uku da APC tayi tana gudanar zaben fidda gwani yazo karshe yayin da jam’iyyar ta fara tantance kuri’un da deliget guda 2,322 sukka kada a zaben da aka kammala da misalin karfe 7:30 na safe.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bar filin zaben ne tun karfe 1:20 na dare inda kafin ya tafi ya yayi kira ga ‘yan takarar cewa su gudanar da zaben cikin limana.
A baya shugaban jam’iyyar Abdullahi Adamu yaso ya hada rikici bayan daya zabi mutun guda a maysayin dan takarar APC, amma gwamnoni 11 na Arewa sun tashi tsaye sun goyi bayan Kudu dari bisa dari.
Yayin da yanzu jagaban, Tinubu da Osinbajo da Amaechi ke kan gaba a zaben, bayan da gwamna Fayemi, Gwamna Badaru da sauransu suka janyewa Tinubu.