fbpx
Tuesday, September 29
Shadow

Hotuna: Ta kashe Mijinta kwanaki 11 bayan auren a yayin da yazo yin kwanciyar aure da ita a Bauchi

Rahotanni daga jihar Bauchi na cewa wata mata, karamar yarinya da bata kai shekaru 20 ba, ta kashe mijinta kwanaki 11 bayan aurensu.

 

Matar me shekaru 18 me suna Salma Hassan ta kashe mijinta, Muhammad Mustapha saboda rashin fahimtar da suka samu yayin da yazo kwanciyar aure da ita.

Salma ta gayawa Daily Sun cewa ta cakawa mijin nata wukane yayin da yazo kwanciya da ita amma tace masa bata yadda ba amma ya nace.

 

Tace suna son junansu kuma kwanaki 11 kenan da Aurensu, tae yazo kwanciya da ita sai ta kiya, dalilin hakane ya daketa ita kuma sai ta dauko wuka, tace kawai ta dauko wukarne dan ta batsoro amma bata yi niyyar kasheshi ba.

Kadan na caka masa a kirji,Ban san Zai mutu ba, na yi nadamar abinda na yi kuma ina cikin bakin ciki, yanzu bansan abinda zai faru daniba,yarinyar ta fada tana sheshshekar kuka.

 

Kwamishinan ‘yansandan jihar,Philip Magu ya bayyana cewa Salma ta aikata kisanne a Ranar 24 ga watan Afrilu inda kuma tuni ta amsa laifinta.

 

Yace a lokacin data cakawa mijin nata wuka, an garzaya dashi Asibitin Itas Gadau, Garin da lamarin ya faru amma tuni ya mutu, yace wani Haruna Musane ya kaiwa ‘yansandan garin rahoton lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *