Rahotanni daga johar Cross-Rivers sun bayyana cewa, Kwamishinan muhalli na jihar tare da wasu ma’aikatan kare muhalli sun shiga gari suna kwace kayan masu kananan sana’o’i dake zaune a bakin hanya suna zubawa a cikin wata babbar motar daukar kaya da suke tafe da ita.
Wannan matar wadda aka kwacewa kayan sana’arta da aka kiyasta kudinsu basu wuce naira dubu biyarba, ta shiga karkashin motar da aka zuba kayan nata tana kururuwar cewa indai ba’a mayar mata da kayan sana’ar nata ba to saidai motar tabi ta kanta.
Rahotanni sun bayyana cewa saida mutane suka hadu aka baiwa matar hakuri sannan ta yarda ta fito daga karkashin motar.