Idan Allah ya kaimu gobe shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sauka a garin Kano dan yin ziyarar aiki ta kwana biyu, an dai jima ana tsammanin zuwan Buharin jihar ta Kano, jihar data bashi kuri’a mafi yawa a zaben shekarar 2015, me baiwa shugaban kasar shawara ta fannin sabbin kafafen sadarwa, Bashir Ahmad ya kara tabbatar da zuwan shugaba Buharin Kano a yau.
Wannan shine karon farko da shugaban kasar zaikai ziya jihar Kanon tun bayan daya lashe zaben shekarar 2015.
Bashir Ahmad ya wallafa sako a dandalinshi na sada zumunta dake cewa “Shugaban kasa Muhammadu Buhari zaikai ziyayar aiki ta kwana biyu, garin da yake da magoya baya mafi yawa, watau jihar Kano”
Muna fatan Allah ya kaishi lafiya.