Gwamnatin tarayya tace wasu bata garin jami’an tsaro na hada kai da masu laifi ana satar danyen man fetur a yankin Naija Delta.
Karamin ministan mai, Timipre Sylva ne ya bayyana haka a ganawar da yayi da manema labarai.
Yace gwamnati na kokarin ganin tana saka ido sosai kan jami’an tsaron da aka baiwa aikin tsare harkar danyen man.
Yace idan aka kai jami’in tsaro ya hana laifi amma ba’a saka mai ido aga yana aikin yanda ya kamata, yana iya rikidewa shima ya zama me laifin.
Ya kara da cewa kuma satar danyen mai a Najeriya ba a yau aka fara ba, ko kuma ba a gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari aka fara yinta ba, yace ta dade ana yi.