fbpx
Saturday, June 10
Shadow

Tafiya me Hadari: Kalli Tawagar motocin gwamna Tambuwal akan kwale-kwale suna tsallaka ruwa

Tawagar motocin gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato kenan jiya, Laraba, a cikin jirgin kwale-kwale lokcin da suke tsallaka ruwa zuwa karamar hukumar Ibi dake jihar Taraba inda zasuyi gaisuwar mahaifiyar dan majalisar tarayya, Isiyaka Bawa, Hajiya Hadiza.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Za’a iya hango Gwamnan a daya daga cikin hotunan yana leko kai ta tagar motarshi, saida suka dauki mintuna talatin suna tafiya akan ruwan, wanda da yawa suka fassarata da tafiya me hadari. Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan siyasa sunyi ta alkawarin gina gada da zata saukakawa mutane tsallaka ruwan cikin sauki amma shekaru hamsin kenan da wannan alkawari har yanzu babu labari.
Daga dandalin sada zumunta da muhawara na jihar gwamnatin Sakkwato.
Mutane da dama sun yita bayyana mabanbanta ra’ayoyi akan wadannan hotuna da suka bayyana, yawanci dai mamaki abin ya bayar domin da yawa basuyi tunanin gwamna guda zai yarda yayi irin wannan tafiya me cike da hadari ba.
Wasu kuma cewa suka rikayi hakan yayi daidai, gara suma manyan su rika jin irin yanda talakawa sukeji.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Tinubu ya gana da sarakunan gargajiya a fadarsa

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *