fbpx
Thursday, June 8
Shadow

Tag: A. A Rano

A. A Rano Zai Fara Hakar Sufurin Jiragen Sama

A. A Rano Zai Fara Hakar Sufurin Jiragen Sama

Kasuwanci
Wasu rahotonni suna nuna cewa hamshakin dan kasuwar man fetur da ke jihar Kano, Alhaji Auwalu Abdullahi Rano ya shirya tsaf domin fara kasuwancin sufurin jiragen Sama. Auwalu Rano wanda aka fi sani da A. A Rano zai fara harkar sufurin jiragen da sunan Rano Air Limited. Tuni dai shirye-shirye neman lasisi daga hukumar kula zirga-zirgar jiragen sama ta ƙasa NCAA ya yi nisa, wanda hakan zai bayar da damar tsara jadawalin yadda fasinjoji da kuma daukar kaya za su kasance. Manema labarai sunyi kokarin jin ta bakin Alhaji Auwalu Rano abin ya ci tura, sai dai wani makusancinsa ya tabbatar da cewa A.A Rano ya baiwa harkar sufurin jiragen saman muhimmancin gaske.