fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Tag: A daidaita Sahu

Masu A daidaita Sahu Sun Fara Yajin Aiki a Jihar Kano

Masu A daidaita Sahu Sun Fara Yajin Aiki a Jihar Kano

Siyasa
Fasinjoji a cikin garin na kano sun kasance cikin rudani biyo bayan fara yajin aikin na sai baba-ta-gani da masu kekenapep suka fara, wanda akasari ake kira Adaidaita Sahu, a jihar a ranar Litinin. Sun shiga yajin aikin ne don kin biyan harajin N100 da gwamnatin jihar ta sanya ta hanyar Hukumar Kula da Hanyoyi da Motoci ta Jihar Kano (KAROTA) da sauran batutuwa. Sun ce matakin ya zama dole don kauce wa abin da suka bayyana da kwace da sunan haraji da sauran tarar. Yawancin tituna a cikin birni sun kasance ba kowa sai dai motoci masu zaman kansu, motocin safa, motocin haya, babura, da manyan motoci ke bin hanyoyin. Aminiya ta ruwaito cewa mafi yawan matafiya masu matsakaicin matsayi da ke zuwa wuraren ayyukansu da kuma daliban da ke zuwa makaranta sun koma yin tattaki don ...