fbpx
Thursday, May 19
Shadow

Tag: AA Rano

AA Rano ya jajantawa ‘yan Najeriya bisa rasuwar Sarkin Zazzau

AA Rano ya jajantawa ‘yan Najeriya bisa rasuwar Sarkin Zazzau

Uncategorized
Shugaban kamfanin AA Rano Nigeria Limited, Alhaji Auwalu Abdullahi Rano (AA Rano) ya jajantawa masarautar Zazzau, da masarautar Rano da Masarautar Kano, da kuma masana’antar mai da iskar gas ta kasa, dama dukkan gwamnatocin jihohi, gwamnatin tarayya da sauran al’ummar Najeriya bisa rasuwar Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris.   Alhaji Shehu Idris ya rasu yana da shekara 84 a wani Asibiti da ke Kaduna bayan gajeruwar jinya inda a kai jana'izarsa a ranar , Lahadi da yamma.   A wata sanarwa ta ta'aziyya wacce mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Sadik Muhammad ya sanya wa hannu, AA Rano ya ce, za a ci gaba da tunawa da Sarkin Zazzau da kuma girmama shi bisa irin dimbin gudunmawar da ya kawo ga kasa baki daya.