fbpx
Friday, December 2
Shadow

Tag: Abba Kabir Yusuf

Kotu ta dage karan da Abba Gida-Gida ya shigar kan Gwamna Ganduje

Kotu ta dage karan da Abba Gida-Gida ya shigar kan Gwamna Ganduje

Uncategorized
Rahotanni daga jihar Kano sun bayyana cewa kotun jihar ta dage karar da dan takarar Gwamna na jam'iyyar PDP a zaben shekarar 2019, Abba K Yusuf ya shigar da gwamnatin jihar inda yake kalubalantar sayar da wasu kadarorin jihar.   Lauyan Abba, Bashir Yusuf Tudun Wazirci ya bayyanawa kotun cewa sayar da kadarorin da gwamnatin jihar taje ya sabawa doka. Saidai wakilin Gwamnati kuma kwamishinan shari'a, Barista Musa Abdullahi Lawal ya bayyana cewa wannan ikirari bashi da tushe ballantana makama. Mai shari'a Nura Sagir ya dage sauraren karar zuwa 29 ga watan Octoba, kamar yanda Freedomradio ta ruwaito.
Dambarwa: Abba Kabir Yusuf ya shigar da Ganduje kara bisa zargin karkatar da Otal din Daula ga wani Dankasuwa a jihar Kano

Dambarwa: Abba Kabir Yusuf ya shigar da Ganduje kara bisa zargin karkatar da Otal din Daula ga wani Dankasuwa a jihar Kano

Siyasa
Da'alamu siyasar Kano ta fara daukan wani sabon salo, wanda a 'yan kwanakin nan anjiyo ita kanta kungiyar kwankwasiyya ta kai karar gwamnatin jihar Kano bisa kudirinta na samar da jirgin kasa a cikin birnin jihar wanda gwamnatin jihar ta shirya ciyo bashin sa. Shima dan Takarar jam'iyyar PDP a shekarar 2019 Abba Kabir Yusuf ya shigar da gwmanatin jihar kano kara, inda yake zargin cewa gwamnatin ta ware wasu gine-gine mallakar jihar ga wasu 'yan kasuwa a jihar. Gine-ginan dai sun hada da Otel din Daula wanda gwamnatin ta mallakawa wani Dankasuwa Da ya shahara A jihar Muddansir Idris, haka zalika gwamnatin ta mallakawa wani Dankasuwa wajan ajiye motoci na Shahuci ga wani Dankasuwa Al-Samad. Dan takarar gwamnan na Jam'iyyar PDP ya bayar da hujjar cewa matakin da gwamnatin jihar Kano ...