
Kotun tarayya ta bayar da umurni akai DCP Abba Kyari gidan yari, bayan taki bada belinsa
Babban kotun tarayya dake jihar Abuja taki bayar da belin DCP Abba Kyari da sauran yaransa, wanda ake tuhuma da laifin harkallar miyagin kwayoyi.
Inda kotun ta bayar da umurni cewa a kai Abba Kyari gidan yari tare da sauran nasa bayan taki bayar da belin nasa.
Kuma tace taki bayar da belin saboda hukumar EFCC ta bayar da kwararan hujjoji akan zargin da ake yiwa dakataccen jami'in dan sandan.