fbpx
Wednesday, May 25
Shadow

Tag: Abdulaziz Yari

Kotu ta yi watsi da neman EFCC ta binciki tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari kan batan Biliyan 900

Kotu ta yi watsi da neman EFCC ta binciki tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari kan batan Biliyan 900

Uncategorized
Kotun tarayya dake Abuja ta yi watsi da Bukatar saka EFCC ta binciki tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdul'aziz Yari kan zargin batan Naira Biliyan 900.   Mai Shari'a Okon Abang ne ya bayyana haka zaman kotun na ranar Alhamis inda yace bukatar bata samar da cikakkun bayanan da ake bukata ba.   Sannan kuma an makara wajan gabatar da ita.  
Tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari ya mayarwa da gwamnatin Tarayya Miliyan 24 da aka gano a Asusunsa kuma ya kasa bayanin inda ya samesu

Tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari ya mayarwa da gwamnatin Tarayya Miliyan 24 da aka gano a Asusunsa kuma ya kasa bayanin inda ya samesu

Siyasa
Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari mayarwa da gwanatin tarayya, Dala 669 248, Kwatankwacin Naira Miliyan 24.3 da aka gano a Asusunsa na banki.   Babbar kotum gwamnatin tarayya ce ta kwace kudin ta mayarwa gwanatin tarayya a zaman da ta yi a Abuja.   Mai  shari'a Ijeoma Ojukwu ce ta amince da wannan bukata da hukumar hana rashawa ta ICPC ta gabatar mata inda tace Yari ya kasa mata gamsashshen bayanin dalilin da zai sa kada a kwace masa kudin. The final forfeiture order wass made today by the Federal High Court, Abuja.   Justice Ijeoma Ojukwu, in a judgment, held that the former governor had not shown good cause why the order sought by the Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission (ICPC) should not be granted.
Gwamnatin jihar Zamfara ta zargi tsohon gwamnan jihar, Abdulaziz Yari da karkatar da Biliyan 10.8

Gwamnatin jihar Zamfara ta zargi tsohon gwamnan jihar, Abdulaziz Yari da karkatar da Biliyan 10.8

Siyasa
Gwamnatin jihar Zamfara ta zargi tsohon gwamnan jihar, Abdulaziz Yari da karkatar da Biliyan 10.8 na aikin ginin jami'ar gwamnatin jihar.   Kwamishinan kudi na jihar, Rabiu Garba ne ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a Gusau, jiya, Talata. Kamfanin dillancin labaran Najeriya,NAN ya ruwaito kwamishinan na cewa tsohuwar gwamnatin jihar ta karkatar da Biliyan 10.8 daga cikin Biliyan 37 da gwamnatin tarayya ta mayarwa jihar a wancan lokaci.   Ya bayyana cewa kudin na ginin wasu titunan gwamnatin tarayya ne kuma an rika kwasarsu a hankali da Biliyan 5 sannan an kuma kwashe wata Miliyan 850 ranar 9 ga watan Mayu na 2019.   Yace kudin da aka karkatar an kaisu inda abinda aka yi dasu bashi da alaka da gina jami'a a jihar.
Dan kudu APC zata tsayar takarar shugaban kasa a 2023>>Tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari

Dan kudu APC zata tsayar takarar shugaban kasa a 2023>>Tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari

Siyasa
Tsohon gwamman Zamfara, Abdulaziz Yari ya bayyana cewa dan kudu jam'iyyarsu ta APC zata tsayar a matsayin dan takarar shugaban kasa a zaben 2023.   Ya bayyana hakane a wata ganawa da yayi a manema labarai. Yace idan shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya kammala mulkinsa, APC dan kudu zata tsaida a matsayin dan takarar shugaban kasa. Yace amma kuma idan haka ta tabbata to bisa al'ada shugabancin jam'iyyar zai komo yankin Arewa. Yace to zai nemi shugabancin jam'iyyar.   Da aka tambayeshi ko wa yake ganin za'a tsayar a matsayin dan takarar daga kudu? Tsohin shugaban kungiyar gwamnonin ya bayyana cewa ba zai iya fada ba, kar ya batawa wasu rai, yace jam'iyyace ke da wannan alhakin.
Ban karya dokar Coronavirus/COVID-19 ba>>Tsohon Gwamnan Zamfara, Yari ya karyata FAAN

Ban karya dokar Coronavirus/COVID-19 ba>>Tsohon Gwamnan Zamfara, Yari ya karyata FAAN

Siyasa
Tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari ya karyata zargin da hukumar kula da filayen jiragen saman Najeriya, FAAN ta mai na cewa ya ci zarafin daya daga cikin ma'aikatanta sannan kuma ya karya dokar Coronavirus/COVID-19.   Da yake mayar da Martani ta bakin me magana da yawunsa, Mayowa Oluwabiyi yace ba gaskiya bane, be karya kowace dokar Coronavirus/COVID-19 ba a filin jirgin Kano ba. FAAN ta zargi Yari da kin yadda a gwada zafin jikinshi inda yace shi babban Mutum ne(Mutum na Musamman).   Saidai yace yana neman FAAN ta janye wannan zargi data masa sannan kuma ta bashi hakuri.
Hukumar kula da filayan jirgin sama tayi Allah wadai da keta ka’idar matakan kariya da Tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari yayi a filin jirgin Malam Aminu Kano

Hukumar kula da filayan jirgin sama tayi Allah wadai da keta ka’idar matakan kariya da Tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari yayi a filin jirgin Malam Aminu Kano

Kiwon Lafiya
Hukumar kula da filayan jiragen sama ta kasa ta bayyana rashin jin dadinta da wani tsohon gwamnan ya nuna a filin tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano bisa bijerewa matakan kariya na kiwan lafiya da aka sanya a dukkan filayan jiragen saman kasar ga masu tafiye tafiye don dakile yaduwar cutar Coronavirus. Tun dai da fari hukumar ta bayyana cewa Tsohon gwamnan Jihar Zamfara Abdul'aziz Yari a ranar 11 ga watan Yuli, a dai dai lokacin da tsohon gwamnan da sauran matafiya ke kokarin tashi ta filin jirgin saman Malam Aminu Kano dake jihar Kano, amma sai gashi Gwamnan yaki bin ka'idar da aka sanya na matakan kariya wanda Jami'ai dake harabar tashar ke kokarin yi domin kare shauran matafiya dake shirin tafiya. A cewar Hukumar. Hukumar ta kuma bayyana cewa tsohon gwmanna ya bijire wa ka'id...
Dokar hana zirga-zirga bata hana yaduwar Coronavirus ba, ya kamata a sassauta dokar>>Tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari

Dokar hana zirga-zirga bata hana yaduwar Coronavirus ba, ya kamata a sassauta dokar>>Tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari

Kiwon Lafiya
Tsohon hwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ya bayyana cewa dokar hana zirga-zirga da aka saka a jihohin Ogun da Legas da babbanbhornin tarayya Abuja bata hana cutar Coronavirus/COVID-19 yaduwa ba.   Tsohon gwamnan yace ya kamata a sassauta dokar saboda sauran ayyukan tattalin arziki su dawo.   Yari yace rashin sassauta dokar zai saka mutane cikin matsi wanda hakan ka iya haifar da rashin yiwa dokar biyayya.   Ya bayyana hakane a wata sanarwa daya fitar ta hannun me magana da yawunsa, Mr. Mayowa Olubiwuyi.   Yari yace ana iya mayar da saka abin rufe hanci ya zama dole da kuma kula da wanke hannu da nesa-nesa da jina.   Ya kuma bayyana cewa akwai bukatar a rika daukar matakai iri daya na kawar da cutar.   Saidai yari ya ...