fbpx
Friday, December 2
Shadow

Tag: Abdullahi Umar Ganduje

Ganduje ya mika mulkin Kano ga mataimakinsa bayan ya tafi kasar larabawa ta UAE

Ganduje ya mika mulkin Kano ga mataimakinsa bayan ya tafi kasar larabawa ta UAE

Siyasa
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya mika mulkin jihar ga mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna bayan ya tafi kasar larabawa ta UAE. Kwamishin yada labarai na jihar Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan inda yace Gamduje zai halarci wani babban taro ne a kasar larabawan. Kuma yana kira ga manyan jihar da shuwagabanni dasu baiwa mataimakin nasa hadin kai.  
Tsohon Sarkin Kano Sanusi ya goyi bayan Gwamna Ganduje kan dakatar da Sheikh Abduljabbar daga yin wa’azi a Jihar

Tsohon Sarkin Kano Sanusi ya goyi bayan Gwamna Ganduje kan dakatar da Sheikh Abduljabbar daga yin wa’azi a Jihar

Siyasa
Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi ll, ya yaba wa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje kan hana fitaccen malamin nan, Sheikh Abdujjabar Nasiru-Kabara yin wa'azi a jihar. A ranar laraba da ta gaba ne, Gwamna Ganduje ya hana Malam Abduljabbar Nasiru-Kabara yin wa'azi a jihar, inda ya bada umarnin rufe masallacin sa, wanda ke karamar hukumar Gwale a cikin garin Kano. An bayar da umarnin ne biyo bayan korafe-korafen da ake yi cewa mai wa'azin yana zagin sahabban Annabi Muhammad (S.A.W) a cikin tafsirinsa na addini. Tsohon Sarkin ya yi wannan yabo ne lokacin da yake gabatar da lacca daga Oxford, UK, yana mai cewa shawarar da gwamnatin jihar ta yi na hana Mista Nasiru-Kabara abin a yaba ne kuma ya kamata a goyi bayansa. A cewarsa, Musulmai a Kano masu bin tafarkin "Ahlussuna w...
Jihar Kano ta amince ta daina ragewa ma’aikata Albashi

Jihar Kano ta amince ta daina ragewa ma’aikata Albashi

Siyasa, Uncategorized
Gwamnatin jihar Kano da kwamitin sasanci tsakaninta da ma'aikatan jihar ta daina rage musu Albashi.   Wannan mataki ka iya dakatar da yunkurin yajin aikin da maaikatan suka yi niyyar tsunduma a ciki. Ma'aikatan Jihar sun gargadi gwamnatin jihar ta dakatar da rage musu albashi ko kuma su fara yajin aiki.   Wakilin Kungiyar Kwadago, Kabir Ado Minjibir ya bayyana cewa, gwamnatin ta kuma amince ta ci gaba da biyan ma'aikata akan sabon tsarin mafi karancin Albashi. The government has agreed to stop deduction of workers salaries and pensioners take home henceforth. Government has also agreed to return to minimum wage of N30,600 and pledged beginning from January’s salaries since the FAC allocation is now improved.   “The last resolution is that government ...
Boko Haram na Shigar da Almajirai Cikin Ayyukan Su>>Ganduje

Boko Haram na Shigar da Almajirai Cikin Ayyukan Su>>Ganduje

Siyasa
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce mayakan Boko Haram na da almajirai a matsayin mambobin su daga Arewa. Ganduje, wanda ya yi magana a lokacin kaddamar da littafin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan a ranar Talata a Abuja, ya bayyana batun Almajiri a matsayin babbar matsala ga Arewa. "Babu shakka kungiyar Boko Haram ta yi nasara a Najeriya saboda suna da tushe da cibiyar daukar ma'aikata a cikin Almajirai wadanda ba su da zurfin tunani," in ji Ganduje. Gwamnan ya yaba wa tsohon Shugaban kasar kan gudummawar da ya bayar wajen inganta darajar ilimi a kasar nan, musamman ma, kafa makarantun Almajiri a lokacin mulkinsa. “Jonathan ya fadada kuma ya zurfafa tsarin Almajiri kuma muna gyara tsarin Almajiri a Kano kuma muna samar da karin irin wadannan makarantu a ji...
Ran Gwamna Ganduje ya baci saboda janye mukamin Farfesa da jami’ar kasar Amurka ta bashi, Yace jami’ar ta bashi Hakuri

Ran Gwamna Ganduje ya baci saboda janye mukamin Farfesa da jami’ar kasar Amurka ta bashi, Yace jami’ar ta bashi Hakuri

Siyasa
Rikici ya kaure tsakanin tsakanin gwamnatin Kano da kuma Jami'ar East Carolina da ke Amurka kan batun ba gwamnan jihar matsayin Farfesa. Gwamnatin Kano ta nemi jami'ar ta bayar hakuri kan musanta ba gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje matsayin Farfesa inda ta ce ranta ya ɓaci kan naɗin farfesan da ya so kunyata gwamnan. A makon da ya gabata ne sakataren watsa labarai na jihar Kano, Abba Anwar ya fitar da wata sanarwa da ke cewa Jami'ar East Carolina a Amurka ta ba Ganduje matsayin Farfesa sakamakon abin da ta kira "ƙwarewarsa wurin gudanar da mulki na gari da kuma inganta rayuwar al'umma". Kuma a cewar sanarwar, matsayin Farfesan na gwamnan ya shafi bayar da shawarwari ga ɗalibai masu digiri na uku, da kuma ƙananan malamai. Sai dai daga baya jami'ar ta Amurka ta musanta cewa ta...