Tauraron fina-finan Hausa, Abdul Ilyasu Tantiri ya bayana cewa yayi hadarin mota a hanyar Sokoto.
Saidai yace ya karasa Lafiya, kamar yanda ya bayyana ta shafinsa na Instagram.
https://www.instagram.com/p/CG5Y5njBzYC/?igshid=1c2zc7hyih5o3
Tauraron fina-finan Hausa, Abulmumin Ilyasu ya bayyana cewa barayi sun shafe kwanaki 3 a jere suna kai hari a gidanshi.
Tauraron wanda kuma me shirya fim ne ya bayyana haka a shafinsa na sada zumunta inda ya kara da cewa a rana ta 3 dai sun yi nasarar shiga farfajiyar Gidan.
Saidai basu samu nasarar yi masa komai ba inda ya kara da cewa Allah ya kubutar dashi da iyalansa ya kuma roki masoya da su sakashi a addu'a.
https://www.instagram.com/p/CAzDaKtBdiQ/?igshid=1jvc99xyilqpk
Yankin Arewa maso yammadai na daya daga cikin yankunan da suka fi sauran yankunan kasarnan fama da hare-haren 'yan bindiga.
Muna fatan Allah ya tsare ya kuma kiyaye na gaba.