fbpx
Saturday, May 28
Shadow

Tag: Abdulrahman Abdulrazaq

Gwamnan Kwara ya bayar da Albashinsa ga ‘yan jihar kyauta yace kuma rabawa mutane abinci

Gwamnan Kwara ya bayar da Albashinsa ga ‘yan jihar kyauta yace kuma rabawa mutane abinci

Kiwon Lafiya
Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya bayyana cewa ya bayar da Albashinsa na wata 10 gaba daya ga jihar dan a yaki cutar Coronavirus/COVID-19.   Gwamnan ya bayyana hakane a wata sanarwa daya fitar ta hannun sakataren watsa labaransa, Rauf Ajakaye inda ya kuma bayar da umarnin a fara rabawa al'ummar kayan Abinci gida-gida.   Gwamnan yayi kira ga jama'ar jiharsa da su ci gaba da zama a gida tare da nesa-nesa da juna dan kaucewa yaduwar cutar.   Ya bayyana cewa ya dauki wannan matakine saboda akwai bukatar sadaukarwa a wannan lokacin.   Ya kara da cewa duk da yake cutar bata shiga jiharshi ba amma zai yi dukkan mai yiyuwa dan ganin ya kare al'ummarsa.