
Yanzu-yanzu: Buhari na ganawar sirri da Malami da Sabon shugaban EFCC, Bawa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari na wata ganawar sirri da sabon shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa.
Hakama Ministan Shari'a kuma Babban Lauyan Tarayya (AGF), Abubakar Malami, ya shiga tattaunawar mintuna kadan bayan an fara.
Duk da cewa har yanzu ba a tabbatar da ajandar taron ba har zuwa wannan lokacin, amma ana tunanin cewa zai kasance ne kawai game da bayar da umarni ga sabon shugaban na EFCC.