fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Tag: Abdulrashid Maina

Bayan lauyoyi 2 sun tsere, Lauya na 3 dake kare Abdulrashid Maina ya gayawa Kotu cewa shima yana son ya daina Kareshi amma kotun tace bata yadda ba

Bayan lauyoyi 2 sun tsere, Lauya na 3 dake kare Abdulrashid Maina ya gayawa Kotu cewa shima yana son ya daina Kareshi amma kotun tace bata yadda ba

Uncategorized
Lauyan dake kare tsohon shugaban Hukumar gyaran fansho ta kasa, Abdulrashid Maina me suna Sani Katu(SAN) ya nemi babbar kotun gwamnatin tarayya dake Abuja ta bashi dama ya daina kare Maina.   Saidai Lauyan EFCC, Farouk Abdullah yace bai amince da wannan Roko ba inda yace kotun ta yi watsi dashi saboda ya sabawa sashi na 349(8) na dokar aikata Laifuka ta shekarar 2015.   Lauyan EFCC ya kara da cewa dokar ta bukaci Lauya ya bayar da bukatar sa a Rubuce kwanaki 3 kamin zaman Kotu idan yana son ya daina kare wanda ake zargi.   Lauyan Maina, Katu shima ya amince da wannan korafi, saidai yace ai sun tattauna da lauyan EFCC din a bayan fage kan lamarin.   Amma mai shari'a, Okon Abang yace bai yadda da bukatar Lauyan na daina kare Maina ba dan zai kawowa...
Idan ba’a bada belina na ba akwai yiyuwar in rasa kafata>>Abdulrashid Maina

Idan ba’a bada belina na ba akwai yiyuwar in rasa kafata>>Abdulrashid Maina

Siyasa
Tsohon shugaban hukumar gyaran Fansho ta kasa, Abdulrashid Maina ya roki kotu data bada Belinsa saboda matsalar rashin lafiya da yake fama da ita.   Maina yayi wannan roko ne ta bakin lauyansa, Sani Katu SAN a ci gaba da sauraren shari'arsa da ake a ranar 19 ga watan Fabrairu.   Yace an kaishi Asibitin koyarwa na jami'ar Abuja kuma takardar ganin Likitan da yayi na nan a matsayin shaida. Yace Asibitin gidan yarin Kuje da yake bashi sa isassun kayan aiki kuma idan ba'a bada belinsa ba, Zai iya rasa kafarsa.
Jami’an tsaro sun kamo dan Abdulrashid Maina,  Faisal da shima ya tsere

Jami’an tsaro sun kamo dan Abdulrashid Maina, Faisal da shima ya tsere

Tsaro
Dan gidan tsohon shugaban hukumar gyaran Fansho, Abdulrashid Maina wanda ake kira da Faisal shima ya shiga hannu bayan neman da aka mai ruwa a jallo.   EFCC ta bayyanawa kotu cewa an kama dan shekaru 21 din bayan tserewar da yayi bayan da aka bayar da belinsa. An kamashine ranar Laraba. Shima dai Faisal, kamar mahaifinsa yana fuskantar zargin Almundahana akan zarge-zarge 3.
Hotuna da Duminsu:Abdulrashid Maina ya yanke jiki ya fadi

Hotuna da Duminsu:Abdulrashid Maina ya yanke jiki ya fadi

Uncategorized
Tsohon shugaban hukumar gyaran Fansho ta kasa, Abdulrashid Maina ya yanke jiki ya fadi a kotu ana tsaka da shari'arsa.   Gwamnatin tarayya na tuhumar Maina kan zargin Almundahanar Biliyan 2 na kudin Fansho. Lauyansa ya nemi kotu ta bashi damar duba takardun shari'ar dan shigar da neman rashin aikata laifi, shine kawai sai aka ji Maina ya yanke jiki ya fadi.   Hakan yasa dole Kotu ta dakata da shari'ar dan baiwa ma'aikatan gidan yari damar kula dashi.
Babu wata hujja da zata sa na amsa zarge-zargen da ake yi min>>Maina

Babu wata hujja da zata sa na amsa zarge-zargen da ake yi min>>Maina

Siyasa
Abdulrasheed Maina, tsohon Shugaban Kwamitin Rikita-garambawul na Hukumar fansho (PRTT), a ranar Laraba, ya fada wa Babban Kotun Tarayya, Abuja, cewa ba shi da wata hujja da zai amsa a kan tuhumar da Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta'anci (EFCC) ta yi masa.   Maina, wanda ya fada wa mai shari’a Okon Abang jim kadan bayan EFCC, ta bakin lauyanta, Farouk Abdullah, ya rufe kararta, ya ce zai gabatar da bukatar ba da karar. Tsohon shugaban fanshon da aka yiwa garambawul, ta hannun lauyan sa, Anayo Adibe, ya bayyana aniyar sa jim kadan bayan ya tsallake shaidun mai gabatar da kara na tara (PW9), Rouqquaya Ibrahim, mai binciken EFCC.   Mai shari'a Abang ya dage sauraron karar har zuwa ranar Juma'a (10 ga Disamba) don lauyan wanda ake kara, Adobe, ya yi ma...
Shima Sanata Ali Ndume ya yanje daga tsayawa Abdulrashid Maina

Shima Sanata Ali Ndume ya yanje daga tsayawa Abdulrashid Maina

Siyasa
Sanata Ali Ndume dake wakiltar Bono ta kudu a majalitar dattijai ya bayyana rashin dacewar tsayawa Abdulrashid Maina akan zargin da ake masa.   Sanata Ndume ya bayyana cewa ya sanar da Lauyansa, su nemi janyewa daga karar. Ndume bayan da ya tsayawa Maina aka bada belinsa, Maina ya tsere wanda hakan yasa aka saka Ndume a gidan yari sai da ya kwana 5 sannan aka bada belinsa.   Bayan zaman Kotu, Ndume ya bayyana cewa yana jinjinawa 'yansandan Najeriya bisa Kawo Maina da suka yo. Kuma hakan ya nuna cewa suna aiki yansa ya kamata.   Yace kuma zai saka lauyansa ya janye daga tsayawa Maina. “I commend the Nigeria Police Force for executing the bench warrant issued on Maina by the federal high court in Abuja,” Ndume said.   “This has shown tha...
Kotu Ta Tsare Abdulrasheed Maina a Gidan Gyaran Hali Na Kuje

Kotu Ta Tsare Abdulrasheed Maina a Gidan Gyaran Hali Na Kuje

Siyasa
Mai shari’a Okon Abang na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare Abdulrasheed Maina a gidan gyaran hali na Kuje har sai an kammala shari’ar tasa. A ci gaba da shari'ar ranar Juma'a, Lauyan da ke wakiltar Maina, Adaji Abel ya janye a hukumance kuma lauyan da Mista Maina ya shigar ya nemi a jinkirta masa domin ba shi damar yin nazarin gaskiyar lamarin. Mai shari’a Abang ya bayar da bukatar dage zaman ne bisa la’akari da cewa wanda ake kara wanda ake ganin ba shi da laifi yana da damar samun wakilcin lauya. Daga nan ya dage karar zuwa ranar 8 ga Disamba don ci gaba da shari'a.
An gano Abdulrashid Maina na da Motocin haya 50 da gidan Alfarma a Dubai

An gano Abdulrashid Maina na da Motocin haya 50 da gidan Alfarma a Dubai

Uncategorized
A jiyane hukumomi suka dawo da tsohon shugaban hukumar gyaran Fansho ta kasa, Abdulrashid Maina gida Najeriya daga inda ya tsere, watau kasar Nijar.   A zaman kotun da aka yi, a ci gaba da shari'ar Maina da ake a babbar kotun tarayya dake Abuja, wata Shaida ta bayyanawa Kotun cewa an gano Naira Miliyan 500 a Asusun ajiyar wani kamfani, Kongolo Dynamic Cleaning Services wanda ke da alaka da Maina.   Hakanan tace an gano Maina na da Asusun ajiyar banki na Dala wanda Dala 460,000 suka shiga Asusunsa yawanci tsabar kudine. Sannan kuma akwai kadarori 32 dake da alaka dashi a Najeriya.   Hakanan an gano Maina na da Kadarori a Dubai da kasar Amurka. A Dubai an gano Maina na da Motocin da ake masa haya Guda 50, sannan kuma yana da gida na Alfarma. “We al...
Hotunan yanda aka dawo da Abdulrashid Maina gida Najeriya daga kasar Nijar

Hotunan yanda aka dawo da Abdulrashid Maina gida Najeriya daga kasar Nijar

Siyasa
A yaune aka dawo da tsohon shugaban hukumar Fansho ta kasa, Abdulrashid Maina da ya tserewa shari'a ya Boye a kasar Nijar zuwa gida Najeriya.   An dawo dashi ta filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe inda hukumar 'yansanda ta bayar da tabbacin cewa za'a ci gaba da shari'arsa a Kotu.   A dazu kunji yanda muka kawo muku cewa lauyan Maina ya nemi dena kareshi saboda bai biyashi kudin aiki ba sannan kuma kotu ta amince da bukatar hakan.