fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Tag: Abdulrashid

Yanda na shafe watanni 6 ina tunanin karbar belin Maina>>Sanata Ndume

Yanda na shafe watanni 6 ina tunanin karbar belin Maina>>Sanata Ndume

Siyasa
Sanata Ali Ndume ya bayyana yadda ya shafe wata shida yana tunanin karbar belin Abdulrashid Maina, tsohon Shugaban Kwamitin Aiki Da Cikawa na Gyaran Fansho (PRT), wanda ke fuskantar zargin ta’ammuli da haramtattun kudade a gaban kotu.   A watan Nuwamban 2019 Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da belin Maina amma ya shafe wata shida a tsare saboda gaza cika sharuddan belin da kotun ta gindaya masa. Karbar belin Abdulrashid Maina da Sanata Ndume ya yi daga baya ya jawo cece-ku-ce. Ndume shi ne Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Borno ta Kudu, inda Maina ya fito.   Ndume wanda shi ne Shugaban Kwamitin Rundunar Sojin Kasa a Majalisar Dattawa ya bayyana wa ‘yan jarida yadda ya shafe wata shida kafin ya amcince ya karbi belin Maina.   Da y...