
Bayan da ya kwashe watanni 3 a kasar Waje, Tsohon Shugaban kasa, Abdulsamal Abubakar ya dawo Najeriya
Rahotanni daga jihar Naija na cewa tsohon shugaban kasa, Abdulsalam Abubakar ya Dawo gida Najeriya bayan shafe watanni 3 a kasar waje.
Tun a jiya, Juma'a ne jami'an tsaro sukawa Filin jirgin sama dake Minna kawanya inda ana jiran dawowar shugaban, saidai be dawo ba sai yau, Asabar da Safe.
Jami'an tsaron sun sake komawa filin jirgin inda a wannan karin suka hana kowa shiga sai iyalan shugaban wanda daga baya yawo aka kuma daukeshi a mota zuwa gidansa.
Rahoton Punch ya bayyana cewa ya dawo cikin koshin Lafiya.