fbpx
Saturday, March 25
Shadow

Tag: Abia

Gwamnan jihar Abia ya jinjinawa sojojin Najeriya da suka kashe tsageran IPOB

Gwamnan jihar Abia ya jinjinawa sojojin Najeriya da suka kashe tsageran IPOB

Tsaro
Gwamnan jihar Abia, Okezie Ipeazu ya jinjinawa sojojin Najeriya da suka kashe wasu tsagera da suka kai musu hari.   Ana zargin dai tsageran IPOB ne suka yi yunkurin kaiwa sojojin harin yayin da sojojin suka kashe 16 daga cikin su kuma suka dakile harin.   Gwamnan yace ya ji dadin wannan nuna bajinta ta Sojoji, kuma yana jawo hankali matasa kada su rika yin irin wannan ganganci. Gov. Ikpeazu Commends Soldiers Over Killing Of "Unknown Gunmen" Governor Okezie Ikpeazu of Abia State has commended Nigerian soldiers for their gallantry in killing some gunmen that attacked them, pledging its commitment to the protection of lives and properties. The State Commissioner for Information, Chief John Okiyi Kalu, who stated this, warned youths of the state not to put th...
Gwamnatin jihar Abia ta garkame Otal sama da 4 sakamakon kin bin ka’idojin cutar Korona mai saurin yaduwa

Gwamnatin jihar Abia ta garkame Otal sama da 4 sakamakon kin bin ka’idojin cutar Korona mai saurin yaduwa

Kiwon Lafiya
Kimanin otal biyar da ke yankin karamar hukumar Aba ta Arewa A Jihar Abia Jami'an dake sanya ido kan bin laduban cutar Coronavirus a jihar ne suka kulle. Rahotanni sun bayyana cewa an garkame Otal-Otal din sabuda sakacin masu su na kin bin umarnin gwamnati data sanya kan cutar Covid-19. Wata majiya ta bayyana cewa wadanda suka ki bin umarnin gwamnatin jihar a kan COVID-19 za a kama su kuma a gurfanar da su a kotun tafi da gidanka. A halin yanzu, gwamnatin jihar Abia ta haramta duk wasu tarukan dare da ayyukan al'adu a jihar. Haka zalika shugaban kwamitin dake yaki da cutar a jihar . Chris Ezem ya gargadi mamallakan otal din jihar da su kiyaye matakan kariya na cutar idan bahaka ba zasu fuskanci tara har ta kimanain dubu 100
Hukumar NSCDC ta cafke mutum 28 bisa zargin fasa bututun mai, a Abia

Hukumar NSCDC ta cafke mutum 28 bisa zargin fasa bututun mai, a Abia

Crime
Hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC), reshen Abia, tace ta cafke mutane 28 da ake zargi da laifin fasa bututun mai da lalata kayan gwamnati ba bisa ka'ida ba daga watan Satumba zuwa yau a jihar. Kwamandan, hukumar Vincent Ogu, shi ne ya bayyana hakan a yayin zantawarsa da manema labarai a Umuahia ranar Talata. Ya ce, 20 daga cikin wadanda ake zargin tuni an gurfanar da su a gaban kotu. Mista Ogu ya ce sauran takwas din, ciki har da hudu da aka kama a ranar Juma'a, ana kan gudanar da bincike a kansu kuma za a gurfanar da su nan gaba kadan.
Babu wadda zamu kara yadda ta zo mana wajan aiki da shigar banza>>Jihar Abia ta yi gargadi

Babu wadda zamu kara yadda ta zo mana wajan aiki da shigar banza>>Jihar Abia ta yi gargadi

Siyasa
Jihar Abia dake kudancin Najeriya ta yi gargadi ga ma'aikatanta cewa ba zata kara yadda wani ko wata ma'aikaciyar jihar suje wajan aiki da shigar Banza ba.   Hakan ya fito ne daga bakin shugaban ma'aikatan jihar, Onyii Wamah a wajan taron tabbatar da karin girma da aka yi ranar Asabar din data gabata.   Yace masu askin banza da kuma wanda ke wa gashin kansu rini ya koma wata kala an basu nan da Litinin(yau) su cireshi ko kuma su fuskanci fushin Hukuma.   Yace ba zasu bari wajan aiki ya zama gurin da bashi da kima ba ko kuma inda kowa zai yi abinda ya ga dama ba. ABIA State civil workforce has been warned that indecent/shabby dressings would no longer be condoned in the service. The state Head of Service, Onyii Wamah, who spoke on Saturday during t...
Gwamnati zata gina masana’antun kera takalma da suturu a Abia da Kano

Gwamnati zata gina masana’antun kera takalma da suturu a Abia da Kano

Siyasa
Ministan cikin gida a Najeriya, Rauf Aregbesola, ya ce taron majalisar ministoci ya amince a kafa masana'antu biyu na ƙera takalma da sutura da sarafa leda a Janguza da ke Kano da Aba a Jahar Abia karkashin yarjejeniyar hadin-gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu. Ministan ya shaidawa ƴan jarida cewa kamfanonin Najeriya ne za su aiwatar da shirin da taimakon kawaancen China. Aregbesola ya ce aikin zai samar da ayyuka 4,330 ga ƴan kasa baya ga kuɗaɗe N5.1bn na hannun jari.
An kashe sojoji 2 da dansanda 1 a jihar Abia

An kashe sojoji 2 da dansanda 1 a jihar Abia

Uncategorized
Rahotanni daga jihar Abia na cewa wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su wanene ba sun kashe sojoji 2 dake 14 Bridge, Ohafia.   Lamarin ya farune ranar Lahadin data gabata a Owaza dake Ukwa West a jihar Abia. Hakanan shima wani dansandan Najeriya ya rasa ransa bayan da wasu gungun 'yan Bindiga suka kaiwa wani shingen 'yansanda hari a garin Aba.   Kakakin 'yansandan jihar, Geoffrey Ogbonna ya tabbatar da hatin inda yace an kashe 2 daga cikin maharan tare da kama mutum 1 sannan maharan sun tsere da bindigar dansandan da suka kashe, kamar yanda Daily Trust ta ruwaito.   Kwamishinan yada labarai na jihar, John Okiyi ya bayyana cewa gwamnan jihar, Okezie Ikpeazu ya bada umarnin kamo wanda suka aikata wannan aika-aika da kuma kwato bindigar dansandan da suka ...
‘Yan sanda sun kama wadanda ake zargi da satar mutane a jihar a Abia

‘Yan sanda sun kama wadanda ake zargi da satar mutane a jihar a Abia

Tsaro
Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Abia ta tabbatar da kama wasu mutane hudu da ake zargi da hannu a sace wani da a ke kira da Chekwas Daniel dake jihar Aba. Rundunar ta fitar da sunan Wadanda ake zargi da suka hada da Bright Chinonso, Eze Ernest, Chisom Godwin da Chinoyerem Chineye, wadanda suka yi garkuwa tare da sace wani mutum dake cikin  shagon sa a ranar Talata. Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Janet Agbede ne, ya tabbatar da kamun masu laifin a Umuahia, a ranar Juma’a. A cewar sa bayan hukumar ta kammala bincikenta  zata gurfanar da wadanda ake zargi a kotu, domin su fuskanci hukuncin abun da suka aikata. Tun dai da fari Lamarin ya farune a lokacin da masu satar mutanan suka hangi, Nambar mai shagon rubuce a jikin kofar shagun nashi, sai suka, kira Numbar a lakacin mai shago...
Yanzu-Yanzu: Coronavirus/COVID-19 ta kama gwamnan Abia

Yanzu-Yanzu: Coronavirus/COVID-19 ta kama gwamnan Abia

Kiwon Lafiya
Labarin da muke samu da dumi-dumi na cewa gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu ya kamu da cutar Coronavirus/COVID-19.   Kwamishinan yada labarai na jihar, John Okiyi Kalu ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai da safiyar yau, Litinin. Yace gwamnan ya killace kansa kuma ya bukaci magaimakinsa daya ci gaba da kula da al'amuran mulki har sai abinda hali yayi.