fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Tag: abin dariya

Shugaban kasar Amurka, Trump yace shugaban Koriya ta Arewa, Kim, ya zageshi ta hanyar ce mishi “tsoho” amma ya rama

Uncategorized
 Wani abin dariya da daukar hankali ya faru tsakanin shugaban kasar Amurka Donald J. Trump da takawaranshi da suke yakin cacar baki watau Kim Jong Un na kasar Koriya ta Arewa, Trump dinne yayi wani rubutu a dandalinshi  na sada zumuna da muhawara na shafin Twitter inda yace. "Me zai sa shugaban kasar koriya ta Arewa, Kim Jong Un yace min "Tsoho", wannan ai zagi na yayi, duk da ni kuma bazan taba kiranshi da "gajere, Kato ba"ayya(Na riga na fadi) nayi matukar kokarin ganin cewa mun zama abokai, watakila wataran zamu zama abokan!" Trump dai da Kim suna caccar bakine akan shirin makamin kare dangi da kasar Koriya ta Arewar ke kerawa.

Tijjani Asase da diyarshi sunyi gasar iya gayu, wai kuma shine ya lashe gasar

Uncategorized
Tauraron fina-finan Hausa Tijjani Asase kenan a wannan hoton tare da diyarshi me suna fanna,  jarumin yace a yaune sukayi gasar kwalliya, iya gayu shi da diyar tashi kuma wai shine ya lashe gasar da kuri'a 6 ita kuma tana da kuri'a 4. Abin dai ya nisha dantar amma mutane da yawa da sukayi sharhi akan wannan batu basu yarda da sakamakon gasarba, inda sukace anyi magudi. Gadai abinda Tijjani ya rubuta: " Salam barkanmu da asuba Asafiyar yaune akai gasar iya gayu wato wanka nida 'Yata fanna inda na kasata da kuriya 6 da 4 saikuta yani murna dan tsoho ya kada yarinya." Kalli wasu daga cikin ra'ayoyin mutane akan wannan batu: