fbpx
Tuesday, May 17
Shadow

Tag: abin mamaki

Mutane sun ga duniyoyin Venus da Jupiter a lokaci guda

Uncategorized
An ga Jupiter da Venus, duniyoyi biyu mafi haske, wadanda suka bayyana tare da juna a sararin samaniya da safe. Ana ganin su da ido a sassan Birtaniya da wasu kasashe da ke tsakiya da arewacin duniya, da kuma wani sashe na Amurka. Masana sun ce duniyoyin sun kasance kusa da juna, kamar wasu taurari masu haske. An fi ganinsu a Birtaniya, minti 40 kafin fitowar rana, amma duniyoyin suna fara bayyana ne kafin fitowar Al Fijir. A yayin da ake iya ganinsu da ido, wasu da suka yi amfani da na'urar hangen nesa na iya ganin wasu halittun duniyar Jupiter. Mutanen Birtaniya da dama sun yada hotunan yadda duniyoyin biyu suka bayyana a shafukan sadarwa na Intanet. bbchausa.

Wannan hoton na gwamnan jihar Rivers ya dauki hankula

Uncategorized
Wannan hoton na gwamnan jihar River Nyesom Wike ya dauki hankulan mutane, a jiyane aka dauki hoton bayan da gwamnan ya halarci wani taron jam'iyyar PDP a jihar Enugu, hoton dai ya nuna gwamnan kamar yana jin bacci, wasu kuma da sukayi sharhi a hoton sunce wai yasha giyane ya bugu. Amma wasu sun kareshi inda sukace ai me zirga-zirga da aiki irin na gwamna ba abin mamaki bane idan ma an ganshi yana jin bacci, haka kuma wasu sunce idan ma giyar yasha ai yana da hankalinshi yasan dai-dai yasan ba dai-dai ba.

Kullun kara shiga dawa ake: Ga wani shima da aka mai makara me siffar jirgin sama: Wani kuma aka binneshi da rigar kwat da lasifikar kunne

Uncategorized
Allah sarki, Iska na wahalar da me kayan kara, a jiyane mukaji labarin wani da aka binne da makara da akayiwa siffar gida harda tauraron dan adam to yauma ga wani da aka yiwa makara me siffar jirgin sama, rahotanni sun bayyana cewa wannan lamari ya faru a jihar Cross-Rivers ne kuma ya dauki hankulan mutane sosai. Muma kara godewa Allah da ni'imar Imani da yayi mana, Allah ka tabbatar damu akan gaskiya. Haka shima wannan da ake ganin hotonshi a sama, wani tsohon me shirya kida ne daya mutu kuma aka sakamai rigar kwat da kuma lasifikar kunne za'a binneshi da ita.

Yanda masu zaman gidan kaso a kasar Isra’ila ke dabarar samun haihuwa da matansu ta barauniyar hanya

Uncategorized
A kasar Isra'ila akwai falasdinawa wanda aka yankewa hukuncin zama gidan kaso na tsawon shekaru saboda laifika daban-daban da suka aikata, masu iyali daga cikinsu na yin dabarar fitar da maniyyinsu ta barauniyar hanya dan kaiwa matansu dake can gida, a saka musu a mahaifarsu dan su samu su haihu. Kamar yanda wani me suna mustafa dake zaman gidan kaso yake gayawa wakilin Aljazeera a wata hira da yayi dashi. Ya kara da cewa wannan itace hanya daya tilo da zasu iya kasancewa da matansu ba tare da matan nasu sun manta dasu ba sun samu wasu mazajen sunyi aureba. Shi Mustafa yana da da namiji da matarshi me suna Maya ta haifa mishi ta irin wannan hanyar ta fitar da maniyyinshi ta barauniyar hanya, kuma an sakawa dan nashi suna Assad. Matar wani shima dake zaman gidan kason a kasar Isra'il...