fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Tag: Abinci

Najeriya na fuskantar matsalar Karancin Abinci Saboda kasashen da take siyo Abincin sun fara boyeshi

Najeriya na fuskantar matsalar Karancin Abinci Saboda kasashen da take siyo Abincin sun fara boyeshi

Kasuwanci
Matsalar manyan kasashen Duniya dake ta kokarin tara Abinci na wa Najeriya da sauran kasashen da suka dogara da shigo da Abinci daga kasashen waje Barazanar yunwa.   Zuwan cutar Coronavirus/COVID-19 yasa kasashen da suka ci gaba ke ta kokarin yin tanadin Abinci saboda rashin tabbas na me zai faru nan gaba.   Hakanan hukumar kula da yanayi ta Najeriya, NiMet ta bayyana cewa matsalar sauyin yanayi da kuma ta tsaro na barazana ga manoma ta yamda da wuya a samu yawan abincin da ake so.   Abincin da ake tsammanin zai yi wahala ashine Masara, Alkama, Shinkafa da sauransu, Kamar yanda Guardian ta ruwaito.
Dalilin da yasa farashin kayan abinci ke tashi sosai>>Gwamnati

Dalilin da yasa farashin kayan abinci ke tashi sosai>>Gwamnati

Siyasa
Taron Majalisar Tattalin Arzikin Kasa (NEC) wanda Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta, a ranar Alhamis, ya yi nazari kan yanayin farashin kayan abinci kuma ya kammala cewa farashin na tashi saboda COVID-19, da #EndSARS da 'yan fashi a sassan kasar.   Yace ya lura da wasu dalilai da suka hada da rikicin manoma da makiyaya da karin kudin sufuri. Wannan ya biyo bayan gabatarwar da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkar noma, Dakta Andrew Kwasari ya gabatar wa NEC.   Don haka majalisar ta jaddada bukatar daukar matakan gyara cikin gaggawa.
Matsalar tsaro ce ke kawo wahalar Abinci>>Dattawan Arewa

Matsalar tsaro ce ke kawo wahalar Abinci>>Dattawan Arewa

Uncategorized
Dattawan Arewa sun bayyana cewa matsalar tsaro ce ke kawo karancin Abinci ko kuma tsadarsa.   Dattawan sun yi maganane a karkashin kungiyar su ta CNEPD ta bakin dsya dsga cikin shuwagabannin su, Zana Goni.   Ya bayyana cewa matsalar tsaro na matukar tasiri a harkar tsadsr Abinci inda yace suna kira da a canjawa tsaron Najeriya Fasali.   Yace shuwagabannin tsaro na yanzu da aka nada tun shekarar 2015 a yanzu basa aikin da ya kamata. “The latest killings and abduction along Kaduna-Abuja highway which occurred last Sunday, thus making major headlines in the national dailies did not come to us as a surprise. This is because we are faced daily with this situation, especially in the North East and North West zones of the country”, the Northern elders said....
Ku rika kokari kuna cin abinci me gina jiki saboda zai rika baku kariya daga Coronavirus/COVID-19>>Gwamnati Baiwa ‘yan Najeriya Shawara

Ku rika kokari kuna cin abinci me gina jiki saboda zai rika baku kariya daga Coronavirus/COVID-19>>Gwamnati Baiwa ‘yan Najeriya Shawara

Uncategorized
Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga ’yan Najeriya da su yi amfani da abinci mai gina jiki a matsayin wani babban bangare na dabarun hana ci gaba da yaduwar COVID-19 da gina karfin gwiwar mutane da al’ummomi. Gwamnatin ta kuma jaddada bukatar ba da fifiko ga kasafin kudin da ake warewa bangaren noma da samar da abinci a kasar. Ministar Harkokin Mata, Pauline Tallen, ce ta bayyana hakan a Abuja a ranar Juma'a a wani shiri da kungiyar Action Against Hunger (Nigeria) da kungiyar masu jaddada kayan abinci masu gina jiki a Najeriya suka shirya don tunawa da ranar abinci ta duniya. Tallen, wanda Darakta (Ci gaban Yara) ta wakilta a ma’aikatar, Jummai Mohammed, ta ce kiran ya zama wajibi saboda kalubalen da ke fuskantar Najeriya a yanzu. Ta ce cutar ta COVID-19 da ke yaduwa ta gurgunta h...
Najeriya bata kai karfin ciyar da kanta ba, hana shigo da Binci zai sa abincin ya kara tsada sosai>>Kungiyar Masu masana’antu,MAN

Najeriya bata kai karfin ciyar da kanta ba, hana shigo da Binci zai sa abincin ya kara tsada sosai>>Kungiyar Masu masana’antu,MAN

Kasuwanci, Uncategorized
Kungiyar Masu masana'antu na Najeriya, MAN ta gargadi gwamnati kan cewa bai kamata a hana bayar da dalolin shigo da abinciki kasarnan ba.   Kungiyar ta bakin shugabanta reshen jihar Legas, Ambrose Oruche ta bayyana cewa har yanzu Najeriya bata kai karfin da zata iya samar da abincin da zai ciyar da jama'arta ba. Yace misali Fulawa, Madara da Suga duk ana bukatar a siyosu daga kasashen waje yace amma bai san ta inane gwamnatin ta gano cewa zamu iya ciyar da kan mu ba.   Yace idan aka duba kididdiga ta bayabayannan za'a iya ganin cewa farashin kayan abinci ya tashi wanda hakan ke nuni da yanda neman abincin yafi yawa.