Matar tsohon Gwamnan Oyo, Mrs Florence Ajimobi ta bayyana cewa mutuwar Mijinta, Marigayi Abiola Ajimobi na matukar damunta domin ta yi rashin gwarzo a rayuwa dake karfafa mata gwiwa, masoyi kuma jajirtacce.
Tace amma abinda ke kwantar mata da hankali shine tasan yana can a Aljanna kuma baiwa wata matsala da Ubangiji.
Ta bayyana hakane a lokacin da kungiyar 'yan Jaridu suka je mata ziyara. Tace tana musu goduya kuma duk da mijinta baya nan amma yan cikin zukatansu.
Majalisar Dattawa ta bukaci a sanya wa filin jirgin sama na Ibadan sunan tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Marigayi Sanata Abiola Ajimobi.
Zaman Majalisar na ranar Talata ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta sauya sunan filin jirgin domin tunawa da Ajimobi wanda shi ne Mataimakin Shugaban Marasa Rinjayenta a shekarar 2003 zuwa 2007, a lokacin da ya wakilci mazabar Oyo ta Kudu.
Zauren majalisar ya kuma yi shiru na minti daya domin juyayin rasuwar tsohon gawmnan na Oyo wanda ya rasu a narar 25 ga watan Yuni yana da shekara 70 a duniya sakamakon rashin lafiya.
A ranar Lahadin data gabatane aka yi addu'ar 8, Fidau ta marigayi tsohon gwamnan Oyo, Abiola Ajimobi wanda ya rasu sanadiyyar cutar Coronavirus/COVID-19.
Mataimakin gwamnan jihar, Rauf Olaniyan ya je shiga wajan addu'ar amma jami"an tsaro suka hanashi, dole ya koma inda ya fito.
Daga baya iyalan marigayin sun fitar da sanarwar cewa ba da gangan aka yi hakan ba inda suka ce an bi dokar NCDC ce ta taron mutanen da basu wuce 30 ba wajan addu'ar sannan kuma basu san cewa mataimakin gwamnan zai halarci wajan addu'ar ba shiyasa da mutane 30 suka halarci wajan sai aka kulle kofar, kamar yanda me magana da yawun marigayin, Bolaji Tunji ya bayyanawa manema labarai.
Yace amma da suka samu labarain zuwan mataimakin gwamnan sun hanzarta zuwa bakin kofa dan shigo dashi ...
Diyar gwamnan Kano, Fatima Ganduje wadda mata ce ga dan marigayi tsohon gwamnan Oyo, Idris Ajimobi ta gayawa gwamnan Oyo, Seyi Makinde cewa ba zai taba kamo kafar Marigayi Ajimobi ba wajan nasarori.
Wani me Suna Segun Awosanya ne da aka fi sani da Segalink yayi rubutu a shafinshi na sada zumunta inda ya jinjinawa gwamna Makinde da cewa yayi kokari da bai bari tausai yasa ya manta a cuci mutanen jihar Oyo da cin hanci ba.
Saidai a martaninta, Fatima ta rubuta cewa Seyi Makinde ba zai taba zuwa ko kusa da gwamna Ajimobi ba dan ba sa'ansa bane.
An dai sha dambarwa da iyalan marigayi tsohon gwamnan da kuma gwamnatin jihar musamman wajan maganar binne gawar Ajimobi da kuma cewa gwamnatin jihar bata musu ta'aziyya ba.
A yau ne dai aka binne gawar tshohon gwamanan jihar Oyo kuma suriki ga gwamnan Kano Abdullahi Uamar Ganduje Sanata Abiola Ajimobi.
Rahotanni sun bayyana cewa an binne mamacin ne a wani gidansa, haka zalika al'ummar da sukai jana'izar sa basu wuce 20 ba kamar yadda rahotanni suka shaida.
Sai dai kuma ma'iya cewa Lamarin ya sha bam ban a wajan da ake gudanar da addu'o'I bisa rashin mamacin, inda dandazon jama'a a ke kokawa da juna wajan karbar wasu abubuwa a harabar gidan ba tare da bada wata tazara ba, kasancewar hakan shine ka'idojin da hukumar lafiya ta sanya don kaucewa kamuwa da cutar coronavirus.
https://twitter.com/thecableng/status/1277223516698554372?s=20
https://www.youtube.com/watch?v=9g1HcYAPpUM
Rahotan wanada jaridar TheCable ta rawaito.
Da misalin karfe 10:05 na safiyar yau,Lahadine aka binne gawar marigayi, tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi wanda surukine ga gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje a gidansa dake Yemoje, Ibadan, babban birnin jihar ta Oyo.
Rahotanni sun bayyana cewa mutanen da suka hakarci binne gawar mamacin basu wuce 20 ba wanda suka hada da iyalai da ‘yan uwa na kusa.
Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya halarci sallar Juma'a a masallacin Yarbawa dake Abuja, inda aka gabatar da addu'o'i na musamman bayan idar da Sallah ga sirikin Gwamna Ganduje, tsohon Gwamnan Jihar Oyo Abiola Ajimobi wanda Allah ya yi wa rasuwa a jiya Alhamis.
Gwamna Ganduje na tare da Sanata Kabiru Gaya, da 'yan majalisar taraiya Hon Ado Alhassan Doguwa shugaban masu rinjaye na majalisar, da Hon Alhassan Rurum da kuma shugaban hukumar karbar kurafi na jiha wato Barrister Muhuyi Magaji Rimin Gado, da kuma Hon Faruk Adamu.
Haka kuma wasu gwamnon da jiga-jigan jam'iyyar APC sun kaiwa Gwamna Ganduje ziyarar jajen rasuwar sirikin nasa.
Rahotanni daga jihar Oyo na cewa an dage jana'izar sanata Abiola Ajimobi da aka shirya yi inda danginsa suka ce nan bada jimawa ba zasu fitar da sabuwar sanarwar yanda za'a yi jana'izar tashi.
Me magana da yawun marigayin, Bolaji Tunji ne ya bayyana haka ga manema labarai inda yayi kira ga masu zuwa gaisuwa da su rika bin dokokin wane hannu da nesa-nesa da juna.
Ya kumankara da cewa jana'izar zata zama sai na kusa kawai da marigayin kuma za'a bi dokokin da NCDC ta saka awajan jana'izar.
Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyyar sa ga jama'ar jihar Oyo da iyalan marigayi sanata Abiola Ajimobi da ya rasu yau.
Shugaba Buhari ya bayyana Sanata Ajimobi a matsayin wanda ya bautawa Al'ummarsa sannan kuma ya rasu a lokacin da jam'iyyar APC da Najeriya ke bukatarshi.
Yayi fatan Allah ya jikanshi.