fbpx
Tuesday, May 17
Shadow

Tag: Abubakar Malami

Shugaba Buhari ya Zillewa gayyatar Majalisa: Majalisar Wakilai ba ta da ikon gayyatar Shugaba Buhari>>Ministan Shara’a Malami

Shugaba Buhari ya Zillewa gayyatar Majalisa: Majalisar Wakilai ba ta da ikon gayyatar Shugaba Buhari>>Ministan Shara’a Malami

Siyasa
Ministan Shari'a kuma Babban Lauyan Tarayya, Abubakar Malami ya ce majalisar kasa ba ta da hurumin gayyatar Shugaba Muhammadu Buhari.   Idan za ku iya tuna cewa majalisar wakilai a makon da ya gabata ta zartar da kudurin sammaci ga shugaban kasar kan karuwar matsalar rashin tsaro a kasar. An shirya shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bayyana gaban majalisar dokokin kasar ranar Alhamis amma yanzu ba a tabbatar ko zai mutunta bukatar ba.   A wata sanarwa a ranar Laraba, Malami ya ce baya ga ikon kundin tsarin mulki na majalisar kasa ta gayyaci shugaban kasa kan “amfani da sojojin da yake yi”.
Zai Iya Yiwuwa ‘Yan daba ne suka yi harbi a Lekki Tollgate ba Sojoji ba>>Ministan Shari’a, Abubakar Malami

Zai Iya Yiwuwa ‘Yan daba ne suka yi harbi a Lekki Tollgate ba Sojoji ba>>Ministan Shari’a, Abubakar Malami

Siyasa
Ministan Shari'a, Abubakar Malami, a ranar Litinin ya bayyana cewa wasu 'yan daba wadanda ke sanye da kayan sojoji na iya kasancewa wadanda suka yi harbe-harbe ga masu zanga-zangar EndSARS a kofar Lekki da ke Jihar Legas. Hakan na faruwa ne duk da dumbin shaidar bidiyo da ke nuna ma'aikatan Sojojin Najeriya sun afkawa masu zanga-zangar lumana da harsasai masu rai a wurin a ranar 20 ga Oktoba, 2020. Sojojin sun kuma amince da gudanar da aikin a wurin akan bukatar rokon da gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya masu don zuwa gurin. Da yake magana da manema labarai a Abuja, Malami ya ce ana ci gaba da bincike don gano hakikanin abin da ya faru a kofar Lekki. "Ba za ku iya yin watsi da yiwuwar watakila wasu 'yan daba ne aka shirya don kirkirar wannan lamari ba… hakan za...
Da gaskene Buhari yafi Obasanjo, ‘Yaradua, da Jonathan aiki nesa ba kusa ba>>Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya kare me gidansa

Da gaskene Buhari yafi Obasanjo, ‘Yaradua, da Jonathan aiki nesa ba kusa ba>>Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya kare me gidansa

Siyasa
Ministan shari'a, Abubakar Malami ya kare me gidansa shugaban kasa, Muhammadu Buhari akan ikirarin da yayi a lokacin jawabin ranar 'yanci.   A jawabin na shugaban kasa, ya dora Alhakin tabarbarewar Najeriya a hannun shuwagabannin da suka gabata, musamma  daga 1999, lokacin da Najeriyar ta dawo turbar Dimokradiyya. Malami a yayin da yake karbar bakuncin wasu 'yan Siyasa ya bayyana cewa, Gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta gaji rashin aikin yi daga gwamnatocin da suka gabata sannan kuma ta ida ayyukan da gwamnatocin baya suka fitar da kudi aka fara amma aka wofintar dasu.   Yace gwamnatin tasu ta yi kokari sosai.   Ga jawabin da yayi a Turance:   “Our party has not done too badly. We have great and good stories to tell and that can ...
Ministan Shari’a ya ki amsa gayyatar da kwamitin dake binciken Magu ya masa

Ministan Shari’a ya ki amsa gayyatar da kwamitin dake binciken Magu ya masa

Siyasa
Ministan Shari'a, Abubakar Malami ya ki amsa gayyatar da kwamitin Ayo Salami dake binciken, zargin aikata ba daidai ba da ake wa mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu.   Kwamitin ya gayyaci Malami ne bayan da Magu yayi korafin cewa ya kamata Malamin da yake masa zargin aikata ba daidai ba ya bayyana dan kare zargin da ya masa. Hakanan Magu ya kuma bukaci da a sako dawo da duk wani shaida da ya bayar da shaida akan shari'ar tasa inda yace ba'a bashi damar ganawa da shaidun ba.   Saidai Malami a martaninsa, kamar yanda Sahara Reporters ta samo yace ba zai bayyana a matsayin shaida ba akan zargin da akewa Magu, saidai idan gayyatar a karkashin Umarnin shugaban kasa, Muhammadu Buhari dan girmama dokane.   Ya kuma bayyana cewa, zargin da yawa Ma...
Malami na son dakatar da binciken da EFCC kewa wasu manyan ‘yan Siyasa>>Me baiwa shugaba Buhari shawara kan yaki da rashawa, Sagay yayi zargi

Malami na son dakatar da binciken da EFCC kewa wasu manyan ‘yan Siyasa>>Me baiwa shugaba Buhari shawara kan yaki da rashawa, Sagay yayi zargi

Siyasa, Uncategorized
Me baiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari shawara kan yaki da rashawa, Farfesa Itse Sagay ya bayyana cewa gyaran da ake son yiwa hukumar EFCC bai kamata ba.   Sagay yace ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya kuma Ministan shari'a, Abubakar Malami ne kawai ke son yayi amfani da wannan dama wajan dakatar da binciken da akewa wasu manyan 'yan siyasa a kasarnan. Duk da Sagay bai kira sunan Malami ba amma ya bayyana sunan ofishinsa, yace gyaran bai kamata ba saboda ana son a mayar da EFCC din karkashin ofishin ministan shari'ar sannan kuma shine zai iya nada shugabanta.   Yace wanda suka kirkiro wannan gyara suna so ne su mayar da hukumar irin yanda take aiki kamin zuwan gwamnatin shugaba Buhari a shekarar 2015 inda ake kama karya da abinda aka ga dama.   ...
Gwamnatin tarayya ta amince da kafa wata sabuwar hukumar yaki da cin hanci

Gwamnatin tarayya ta amince da kafa wata sabuwar hukumar yaki da cin hanci

Siyasa
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta amince da kafa wata sabuwar hukumar yaki da cin hanci me suna, proceeds of crime recovery and Management Agency.   Hukumar zata kasance ne tana kula da kadarorin da aka kwato daga barayin gwamnati, kamar yanda ministan shari'a kuma babban lauyan gwamnati,  Abubakar Malami ya bayyanawa manema labarai. Yace a yanzu hukumomi daban-daban ne ke kula da kadarorin da ka kwato amma wannan hukuma itace daga yanzu data rika kula da kadarorin.   Yace majalisar zartaswa ta amince da kudirin inda aka aikewa da majalisar tarayya dan sakashi cikin doka.
Da gaggawa zan amsa gayyatar Kwamitin Ayo Salami>>Malami

Da gaggawa zan amsa gayyatar Kwamitin Ayo Salami>>Malami

Uncategorized
Babban Lauyan gwamnati,  Abubakar Malami ya bayyana cewa ba zai yi wata-wata ba wajan karba gayyatar kwamitin Ayo Salami dake bincikar Magu ba idan aka gayyaceshi ya bada shaida. Malami ya bayyana hakane a hirar da yayi da gidan Talabijin na AriseTV inda yace bashi da wani abu da zai boye dan haka idan aka gayyaceshi zai amsa gayyatar ya kuma fadi abinda ya sani.
Kwamitin dake binciken Magu ya gayyaci Ministan Shari’a, Abubakar Malami

Kwamitin dake binciken Magu ya gayyaci Ministan Shari’a, Abubakar Malami

Uncategorized
Kwamitin dake binciken Dakataccen mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu da tsohon Mai shari'a,  Ayo Salami ke shugabanta ya aikewa Ministan Shari'a kuma babban lauyan Gwamnati bukatar ya bayyana a gabansa.   Kwamitin ya bukaci Salami ya bayyana a gabansa ne dan bada shaida akan zargin da shine tun farko yawa Magu. Ana zargin Magu da aikata ba daidai ba da Dukiyar da aka kwato daga barayin gwamnati wanda ya sha Musantawa.   A baya Lauyan Magu, Wahan Shittu ya bukaci da kwamitin ya gayyaci Minista Malami ya bada shaida kan zargin da yakewa wanda yake karewa.
Dama Can ni me kudi ne kamin ka bani mukami>>Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya gayawa Shugaba Buhari

Dama Can ni me kudi ne kamin ka bani mukami>>Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya gayawa Shugaba Buhari

Siyasa
Ministan Shari'a,  Abubakar Malami ya bayyanawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari cewa dama can shi me kudi ne tun kamin shugaban kasar ya bashi mukamin Minista.   Malamai ya aikewa da shugaban kasa wannan bayanine saboda yanda wasu ke ta kira a tuhumeshi kan Almundahanar Miliyoyin Kudi. A cikin takardar bayanin da ya aikewa shugaban kasar, Malami ya bayyana cewa cikin bayanan da ya bayar kamin ya zama Minista ya saka kadarori 27 da ya mallaka.   Yace wasu daga cikin kasuwancin daya mallaka masu tsoka sune Otal din Rayhaan da Rayhaan Food and Drinks wanda ya mallaka tun a shekarar 2013 kamin ya zama Minista.   Ya kuma bayyana cewa ya kaddamar da matakin shari'a akan wanda suka masa wancan zargin