fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Tag: Abubakar Sa’ad

Mai al’farma sarkin Musulmai yayi Allah wadai da kisan ta’addanci da ‘yan Boko haram da ‘yan bindiga ke kaiwa

Mai al’farma sarkin Musulmai yayi Allah wadai da kisan ta’addanci da ‘yan Boko haram da ‘yan bindiga ke kaiwa

Tsaro
Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma jagoran kungiyar Jamaatu Nasril Islam, Alhaji Sa’ad Abubakar lll, ya yi Allah wadai da kisan gilla da ‘yan ta’addan Boko Haram da’ yan bindiga suke yi a fadin kasar. A cewarsa, ya kamata gwamnatocin tarayya da na jihohi su farka wajen sauke nauyin da ke kansu na kare rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya kamar yadda yake a kundin tsarin mulki. Mai alfarma Sarkin wanda ya yi magana ta bakin Sakatare-janar na JNI, Dr. Khalid Abubakar-Aliyu, a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Kaduna a ranar Laraba, ya kuma umarci al’ummar musulmi da su yi addu’ar Allah ya kawo karshan tashe tashen hankular da suka addabi kasar. Sultan din ya kuma yi Allah wadai da yawaitar matsalar fyade a fadin kasar kuma yayi kira ga gwamnati da ta kare mutuncin mata da...