
Ya saka kanshi a hadari wajan kareni>>Shugaba Buhari ya mika ta’aziyyar Abubakar Tsav
Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya mika ta'aziyyar marigayi tsohon gwamishinan 'yansandan na jihar Legas, Abubakar Tsav.
Ta'aziyyar ta shugaban kasa na kunshene a cikin wani sako daya fitar ta bakin me magana da yawunsa,Malam Garba Shehu.
Shugaba Buhari yace Tsav ya saka kansa cikin hadarin kare gwamnatinsa a koda yaushe. Yace yana mika sakon ta'aziyya ga jama'ar jihar Benue da iyalan mamacin.
Yace irin ci gaba da kwarewar aiki da ya kawo a tsarin aikin 'yansanda zai ci gaba da wazuwa koda bayan bashi.