
Mai tsaron ragar AC Milan Gianluigi Donnarumma na shirin komawa PSG kyauta
Mai tsaron ragar AC Milan da kasar Italiya dan shakara 22 Gianluigi Donnarumma zai bar kungiyar kyauta a karshe wannan watan da zarar kwantirakin shi ya kare.
Kungiyar AC Milan dake fafatawa a gasar Serie A tayi kokarin sabunta kwantirakin dan wasan nata na tsawon wasu watanni amma sun kasa daidaitawa da wakilin shi Mino Riola.
Kuma Paris Saint German na harin siyan golan kyauta inda tayi mai kwantirakin shekaru biyar da albashin yuro miliyan 12 a kowace shekara, kuma zata yi nasarar siyan mai tsaron ragar idan har Barcelona bata karawa mai albashi ba ko kuma ta yi mai kwantiraki kamar irin na PSG.
Donnarumma yanzu yana tare da tawagar kasar shi ta Italiya inda yake shirin gudanar da gwajin lafiyarsa a filin atisayi su na Coverciano, kafin wasan su na farko a gasar Euro wanda zasu...