
Dan Achaba, Hussein ya cinnawa kansa wuta ya mutu saboda ‘yansanda sun kwace mai babur
Wani ɗan achaba a kasar Uganda ya mutu bayan ya cinna wa kansa wuta da nufin nuna fushinsa, bayan `yan sanda sun ƙi ba shi babur ɗinsa da suka kama.
'Yan sanda sun ce dan achaban, mai suna Husseini Walugembe ya bai wa abokinsa ne ɗanin babur ɗin, kuma sai aka yi rashin sa`a `yan sanda suka kama shi da goyon fasinja, alhali an haramta yin haka ƙarƙashin dokokin yaƙi da cutar korona.
An ce takaici ne ya kama dan acaban bayan ya yi ta zuwa ofishin `yan sanda domin su ba shi babur din nasa, amma suka ƙi.
Da ya ga abin ya gagara, sai ya shiga cikin wani daki a harabar ofishin `yan sandan, kana ya kulle ya yayyafa wa jikinsa man fetur din da ya ɗura a cikin wata kwalbar ruwa, sannan ya cinna wa kansa wuta.
`Yan sanda dai sun ce suna gudanar da bincike a kan zargin da ake yi cew...