fbpx
Thursday, May 19
Shadow

Tag: Adaidaita sahu

Da Duminsa: Masu a daidaita sahu a Kano sun amince da biyan harajin Naira 100 kullun, Zasu janye yajin aiki

Da Duminsa: Masu a daidaita sahu a Kano sun amince da biyan harajin Naira 100 kullun, Zasu janye yajin aiki

Siyasa
Rahotannin dake Fitowa daga Jihar Kano na cewa masu a daidaita Sahu sun amince da biyan Harajin Naira 100 a kullun da Gwamnatin jihar ta saka musu.   Shugaban Kungiyar Gwadago na jihar, Kabiru Ado Minjibir ne ya bayyana cewa ana tsammanin masu adaidaita Sahun zasu ci gana da biyan kudin harajin.   Shima Daraktan KAROTA, Baffa Abba Dan Agundi ya bayyana farin cikinsa da wannan hadin kai na masu Adaidaita Sahun, kamar yanda DailyvNews24 ta Ruwaito.
Motocin a Kori kura da Kurkura sun maye gurbin adai-daita sahu a Kano inda suka nunka kudin daukar Fasinja

Motocin a Kori kura da Kurkura sun maye gurbin adai-daita sahu a Kano inda suka nunka kudin daukar Fasinja

Siyasa
Motocin a Kuri kura da Kurkura sun maye gurbin adai-daita sahu a Kano   Tun da safiyar yau ne dai aka wayi gari da yajin aikin masu Adai-daita sahu a jihar Kano inda ya tilastawa mutane da yawa hawa akori kura da domin fita wuraren kasuwanci da ayyukansu na yau da kullum ko kuma mutum ya tafi a kafa.   A zagayen da wakilin Hutudole ya gudanar ta gano yadda mutane ke rigegeniya wajen hawa a kori kura a wurare da dama ko kuma su rasa abin hawa.   Manyan hanyoyin da aka gano masu hawa akori kurar na rububi sun hadar da sabon titin Mandawari zuwa Kwari da Kurna zuwa Ibrahim Taiwo da kuma titin Panshekara zuwa Kofar Fanfo.   Haka zalika an gano wasu akan titin Kofar Ruwa zuwa filin jirgin sama zuwa kasuwar Sabon Gari da wasu tituna daban-daban na ciki...