fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

Tag: adam a. zango

Bidiyo An sake shiryawa Adam A. Zango shagalin Zagayowar ranar haihuwarsa na ban mamaki

Bidiyo An sake shiryawa Adam A. Zango shagalin Zagayowar ranar haihuwarsa na ban mamaki

Nishaɗi
Adam A. Zango ya bayyana cewa an sake shirya masa shagalin murnar zagayowar ranar haihuwarsa na ban mamaki.   Zango ya bayyana hakane ta shafinsa na Instagram inda aka ganshi zaune an gabatar masa da Kek ga kuma masu bushe-bushe.   Yace Maryak KK ce ta shirya masa wannan abu. https://www.instagram.com/p/CGI-TaaHZv_/?igshid=m7hbwpxuhshh   https://www.instagram.com/p/CGJEi6Snhpb/?igshid=y8khlcnymotq    
Bidiyon yanda matar Adam A. Zango ta shirya masa bikin zagayowar ranar haihuwarsa na ban mamaki

Bidiyon yanda matar Adam A. Zango ta shirya masa bikin zagayowar ranar haihuwarsa na ban mamaki

Nishaɗi, Uncategorized
Tauraron fina-finan Hausa kuma Mawaki, Adam A. Zango ya bayyana yanda matarsa, Safiya ta shirya masa bikin ban mamaki na zagayowar ranar haihuwarsa.   Adamu yayi bikin zagayowar ranar haihuwarsa kamar yanda muka kawo muku a baya inda 'yan uwa da abokan arziki suka tayashi Murna.   Adamu ya saka bidiyon yanda matar tasa ta shirya mai wani kasaitacceb biki inda aka yi irin tsarin turawa, sai da aka kulle masa Ido sannan ya je ya gabi. https://youtu.be/WpnsRsafFQY
Adam A. Zango na murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Adam A. Zango na murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Nishaɗi
Tauraron fina-finan Hausa, Adam A. Zango na murnar zagayowar ranar haihuwarsa.   Duk da cewa Adamun bai saka murnar zagayowar ranar haihuwartasa ba a shafinshi na sada zumunta, amma da yawa daga cikin abokan aikinsa na ta tayashi da murna.   Ali Nuhu, Zpretty, Sadiya Haruna da dai sauransu duk sun Taya Adamu Murna. https://www.instagram.com/p/CFx3DMFBOf5/?igshid=1i4hwtzxonyap   Bayan da Ali Nuhu ya taya Adam A. Zango murna inda ya kirashi da Yarima, Adamun ya amsa da cewa na Gode Sarki. https://www.instagram.com/p/CFyFqFEFAIl/?igshid=14ghic7y615vg   https://www.instagram.com/p/CFyBDJdlwNr/?igshid=h3538piawzde    
Ku taya ni da addu’a>>Adam A. Zango ya roki Masoyansa

Ku taya ni da addu’a>>Adam A. Zango ya roki Masoyansa

Nishaɗi
Tauraron Fina-finan Hausa kuma Mawaki, Adam A. Zango ya roki masoyansa da su tayashi da addu'a.   Adamu yayi wannan roko ne ta shafinsa na Instagram saidai be yi karin bayani ba.   Ya saka alamar Damuwa inda yace ku min addu'a. Wasu daga cikin abokan aikinsa sun rika mai fatan Allah ya bashi lafiya. https://www.instagram.com/p/CFfO9PgM-_G/?igshid=1qaprlmja0lde
Munyi Babban Rashi: Ba zan taba mantawa da Sarkin Zazzau ba>>Adam A. Zango

Munyi Babban Rashi: Ba zan taba mantawa da Sarkin Zazzau ba>>Adam A. Zango

Nishaɗi
Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango ya mika sakon ta'aziyyarsa akan rasuwar sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris.   A sakon da ya fitar ta shafinsa na Instagram, Adam A. Zango ya bayyana cewa " Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah ya jikan me martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris. Allah yasa Aljannah Makomarsa. Mun yi babban Rashi. https://www.instagram.com/p/CFXHZmksqZ9/?igshid=kb0erk6k6m5 A wani sako kuma da Adam A. Zango ya sake sakawa akan rasuwar Sarkin Zazzau din ya bayyana cewa, zai ci gaba da godewa sarkin Har Abada. https://www.instagram.com/p/CFYEWmGHv9L/?igshid=5xm62irkyx8r  
Kalli Alamun da suka bayyana cewa Fati Washa ce Adam A. Zango zai aura

Kalli Alamun da suka bayyana cewa Fati Washa ce Adam A. Zango zai aura

Nishaɗi
A baya dai mun kawo muku Rahoton dake cewa Adam A. Zango ya bayyana zai kara aure kuma 'yar Fim ce zai aura.   Adamun ya bayyana hakane ta shafinsa na Instagram saidai daga baya ya goge wannan sako. A baya Adamu da Fati Washa sun sha soyayya wanda kiris ya rage a yi aure amma avin bai tabbata ba. Saidai a yanzu bayan yin waccan maganar tasa, Adamu ya saka hotonsa dana Fati Washa a Profile Picture dinsa na Instagram da alamar zanen Zuciya, dake alamta Soyayya.   Adamun dai bai yi karin haske game da hakan ba, amma lura da maganar da yayi kwanakin baya ana iya cewa watakila Fati Washa din ce zai aura.
Tara Kudin wakar Atiku: Eh Naji Maula Nike kuma sai na tara Miliyan 20 kamin in fara wakar>>Adam A. Zango

Tara Kudin wakar Atiku: Eh Naji Maula Nike kuma sai na tara Miliyan 20 kamin in fara wakar>>Adam A. Zango

Nishaɗi, Uncategorized
Tauraron fina-finan Hausa,  Adam A. Zango ya bayyana cewa duk wanda zasu ce maula yake aje a yi ta fada.   Yace idan wani yayi rawa an bashi kudi, wani kuwa duka zaisha. Adamun yayi wannan rubutu ne a shafinsa na Instagram akan tara kudin yiwa Atiku waka da yake daga masoya.   Ya saka hotunan shaidar tura masa kudin da wasu ke yi. Duk da Adam A. Zango yace daga 500 ne zuwa sama amma a cikin wanda Hutudole ya hango hadda wanda ya aika Naira 5, akwai kuma wanda ya aika Dubu 1.   Adam A Zangon shima dai ya kwaikwayi salon mawakin shugaban kasa, Muhammadu Buhari,  watau Dauda Katutu Rarara inda yace a tara masa kudi yawa Atiku waka dan ya dawo daga Dubai. https://www.instagram.com/p/CFAuWLwD75T/?igshid=17j0tluxo8bp0   https://www.instagram.com/p/C...
Bidiyo: Tunda Aka gama zabe Atiku ya tafi Dubai be dawo ba dan haka ku hada dari 5 mu yi waka dan a kirashi ya dawo>>Adam A. Zango ga masoyan Atiku Abubakar

Bidiyo: Tunda Aka gama zabe Atiku ya tafi Dubai be dawo ba dan haka ku hada dari 5 mu yi waka dan a kirashi ya dawo>>Adam A. Zango ga masoyan Atiku Abubakar

Uncategorized
Bayan da tauraron mawakin shugaban kasa, Muhammadu Buhari,  Dauda Kahutu Rarara ya bukaci masoyan shugaban kasar da su bada tallafin Dubu daidai dan a masa waka ta musamman, shima Adam A. Zago a wani mataki dake nuna Alamar martani ya bukaci da masoyan Atiku Abubakar su tara Dari 5 dan a masa waka.   Adamu a wani sako da ya saki ta shafinsa na sada zumuntar Instagram ya bayyana cewa 'yan Najeriya sun shiga wani hali na matsi wanda a baya ana cewa PDP amma PDP ta yi abinda zata oya ta tafi.   Yace tun bayan da aka gama zabe, Atiku Abubakar ya bar Najeriya ya tafi Dubai bai dawo ba dan haka yake neman a tara kudi dari 5 daga kowane Masoyin Atiku dan a kirashi ya dawo gida Najeriya. https://www.instagram.com/p/CFAWclKjZMg/?igshid=1f4hoeb1gwkym   &nb...