Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki Adam A. Zango ya caccaki wasu wadanda yace suna batamai suna, adamun ya bayyana cewa a baya ya taimakawa mutanen amma yanzu sun koma gefe suna kokarin su bata mai suna saboda haka sun kaishi bango kuma yana da iyali dolene ya tashi tsaye ya kare mutuncin kanshi.
Adamun dai ya bayyana cewa shi ba dan daudu bane kuma baya maula, sannan ya bayyana cewa an mai kazafi da yawa yayi shiru, to wannan karin bazai yi shiru ba, duk da be kira sunaba amma nan gaba idan aka sake yunkurin bata mishi suna to sai ya tonawa mutum asiri.
Adamun dai ya bayyana cewa wasune sukasha alwashin sai sun ga bayanshi.
Gadai kalaman daya rubuta kamar haka:
"Ni ba dan daudu bane kuma ni ba dan maula bane. Sannan ni ba mushiriki bane, bani da malami ko matsafi. D...