
Dan wasan Wolves Adama Traore ya kamu da cutar Covid-19
Adama Traore ba zai yi tafiya izuwa kasar Sifaniya ba domin buga gasar kasashe bayan dan wasan ya kamu da cutar Covid-19. An yiwa gabadaya yan tawagar Luiz Enrique gwajin cutar korona kafin saukar su a sansanin atisayin su dake Los Rozas.
Dan wasan Wolves din ya kasance dan wasan na biyu daya kamu da cutar bayan Mikel Oyarzabal shima ya kamu kafin zuwan su sansanin, saboda haka Traore ba zai samu damar shiga tawagar ba bisa sharuddan da UEFA ta tsara akan yan wasan da suka kamu da annobar.
Kuma hakan na nufin cewa dan wasan ba zai samu damar buga wasan Sifaniya ba har guda biyu wanda zasu buga a watan satumba tsakanin su da kasar Jamus da kuma Ukraine. Wannan ba shine karo na farko da dan wasan mai shekaru 24 ya samu cikas ba wurin buga gasar kasashe, bayan dan wasan ya samu rauni ...